Harin jirgin ƙasa: Na biya N80m ta hannun Tukur Mamu don sako mahaifiyata da ƴan uwana – Shaida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani shaida da iftila’in harin jirgin ƙasa na shekarar 2022 a hanyar Abuja-Kaduna ya rutsa da shi, ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya dake Abuja cewa Naira miliyan 80 ya bai wa ƴan ta’adda a matsayin kuɗin fansa ga mahaifiyarsa da ƴar uwarsa.

A ranar Alhamis, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya gabatar da sauraron ƙarar da aka shigar akan Tukur Mamu, wanda shi ne mai magana da yawun waɗanda suka yi garkuwa da mutanen inda ake tuhumar sa da laifuka 10.

Shaidar ya ce an sako mahaifiyarsa da ƴar uwar tasa ne tare da wasu mutum biyu.

Ya kuma bayyana cewa, a ranar 28 ga watan Maris, 2022 ne aka sanar da shaidan batun garkuwa da ƴan gidansu, waɗanda fasinjoji ne a wani jirgin ƙasa inda aka kashe wasu, raunata wasu da kuma ceto wasu.

Ya ƙara da cewa lambobin ƴan jarida huɗu masu garkuwa da mutanen suka ba shi waɗanda daga cikin su, Tukur Mamu ne kaɗai ya amince a yi magana da shi.

Kazalika, ya bayyana wa kotun cewa a yayin fafutukar ceto mutanen gidan nasu ne wata rana ya samu kira daga tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Lucky Irabor da tsohon Darakta-Janar na hukumar ƴan sandan farin kaya ta SSS, Yusuf Bichi.

Daga nan ne Janar Irabor ya umarci da ya sanar da shi duk abin da suka tattauna da Mamu tare da haɗa shi da kwamitin Gwamantin Tarayya na ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Har’ilayau, bayan doguwar tattaunawa a tsakanin ɓangaren shaidar, Mamu da ƴan bindigar, sai aka cimma matsaya akan biyan N80m wanda Mamu ya umarce shi da ya canza su zuwa Dala tare da ƙara wani karamin adadi a kai a wata Agustan 2022.

A watan Maris na 2023 ne aka kama Mamu bisa laifin taimaka wa ayyukan ta’addanci a Nijeriya.

An zarge shi ne da karɓar kuɗaɗen a hannun iyalan waɗanda aka yi yi garkuwa da su a harin jirgin a madadin ƙungiyar Boko Haram.

Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla wanda ake zargin ya karɓi jimillar Dala 420,000 daga iyalan waɗanda harin ya afaka wa da kuma N21m daga wasu iyalan.

By Babaji