Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mutane biyu suka mutu wasu biyar sun sami mummunan raunuka sakamakon hare haren ‘yan bindiga a kan hanyar Guda zuwa Turare a karamar hukumar Bakori da ke jihar Katsina.

Wata majiya mai tushe ta shaida cewa ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai suka tare hanyar Guda zuwa Turare inda sukai ta kai hare hare akan matafiya da ƙauyukan da ke kan hanyar.

Sai dai bayan samun kiran gaggawa haɗin gwiwa na jami’an tsaro da ke zirga-zirga a kan hanyar suka garzaya zuwa wajen,amma da isar su sun tarar da yan bindiga sun raunata mutane bakwai.

Jami’an tsaron sun garzaya da mutane huɗu wadanda raunukan su ya tsananta zuwa babban asibitin Funtua, sauran mutane uku aka bar su a asibitin Bakori.

Majiyar ya bayyana cewa daga baya mutum biyu daga cikin waɗanda aka kai asibitin Funtua sun rasu sauran mutane biyar na cikin mummunan yanayi.

Wani mazaunin garin Guga ya faɗa cewa mafi yawan Mutanen da hare haren yan bindiga ya shafa a kan hanyar mutanen ƙauyukan Guga da kakumi ne.

A wani labarin kwatankwacin wannan wani ɗauki ba daɗi tsakanin jami’an tsaro da yan bindiga a kauyen kakumi yayi sanadiyar mutuwar mutum ɗaya da raunata jami’in CWC a ƙauyen.

Yanzu haka jami’an tsaron suna kokarin gano maɓoyar ‘yan bindigan a yankin a yanayin da suna cigaba da bincike kamar yadda majiya mai tushe ta faɗa.

By ukarofi