Gwamna Raɗɗa ya buƙaci masu hali su taimaka wajen cigaban al’umma

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya buƙaci masu hannu da shuni a jihar da su riƙa ware wani ɓangare na dukiyar su domin ayyukan jin ƙai da ci gaban al’umma, a matsayin taimako ga ƙoƙarin gwamnati.

Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin ya ke ƙaddamar da wasu ayyuka da wani mai taimakon jama’a, Injiniya Muntari Sagir, ya aiwatar a ƙaramar hukumar Malumfashi.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana ayyukan da Injiniya Muntari Sagir ya aiwatar da suka haɗa da cibiyar kula da lafiya a Al-Makiyayi, ginin ajujuwa uku tare da ofis a kwalejin ungozoma ta Nana Babajo da ke Malumfashi, da kuma bayar da motar bas mai ɗaukar mutane 18 ga makarantar kimiyya ta ’yan mata ta Gwamnati da ke Malumfashi.

Sauran ayyukan da mai taimakon ya aiwatar sun haɗa da magudanar ruwa mai tsawon kilomita ɗaya, kammala katangar maƙabartar Sambo, da kuma gina katanga a makarantar firamare ta Sambo, dukkansu a cikin garin Malumfashi.

Gwamna Raɗɗa ya ce, “Idan ƙarin mutane suka kwaikwayi irin wannan ƙoƙari, nauyin da ke kan gwamnati wajen samar da ababen more rayuwa da ayyukan jin daɗin jama’a zai ragu matuƙa.”

Ya yaba wa Injiniya Sagir bisa gudunmawar da yake bayarwa, tare da ƙarfafa masa gwiwa da ya ci gaba da irin waɗannan ayyuka na jin ƙai.

Ya ƙara da cewa, “Sadaukarwar da ake yi saboda Allah, babu shakka za a saka masa da alheri mai yawa.

“Ina ƙarfafa maka gwiwa ka ci gaba da wannan tafarki na yi wa bil’adama hidima.”inji Dikko.

Gwamna Raɗɗa ya jaddada cewa haɗin gwiwa da masu kishin al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen hanzarta ci gaban al’umma.

Tun da farko, Injiniya Muntari Sagir ya bayyana cewa ya ɗauki nauyin waɗannan ayyuka ne daga kuɗaɗen kasuwancinsa, domin tallafa wa ci gaban al’ummarsa.

Ya ce, “Waɗannan ayyuka wani ɓangare ne na ƙudurina na mayar wa al’umma da abin da na samu, da kuma inganta rayuwar jama’a.”
Ya tabbatar da cewa dukkan cibiyoyin ilimi da na kiwon lafiya da aka samar an tanade su da kayan aiki masu inganci domin ba da kyakkyawan sabis.

Injiniya Sagir ya kuma yi alƙawarin gina katanga a wani maƙabartar da ke bayan makarantar firamare ta Aliyu a Malumfashi.

Haka zalika, babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko ta Jihar, Dr. Shamsuddeen Yahya, ya yaba wa mai taimakon bisa gudunmawarsa a fannin kiwon lafiya cikin shekaru uku da suka gabata.

Ya ce, “Waɗannan ayyuka sun haɗa da kafa ɗakunan gwaje-gwaje, sashen haihuwa, ɓangaren kula da ido, da kuma gyaran wasu cibiyoyin lafiya da dama.”

Ya bayyana waɗannan gudummawa a matsayin masu tasiri da kuma ƙara ƙarfi ga ƙoƙarin gwamnati wajen inganta kiwon lafiya a faɗin jihar.

A nasa ɓangaren, Galadiman Katsina kuma Hakimin Malumfashi, Justice Saddiq Abdullahi Mahuta, ya bayyana cewa gudummawar Injiniya Sagir ba ta tsaya ga fannin kiwon lafiya kaɗai ba.

Ya ambaci gyaran gidan zama na Galadiman Katsina a Malumfashi a matsayin ɗaya daga cikin ayyukan da mai taimakon ya aiwatar.

Ya ce, “Injiniya Sagir ya kasance mai jajircewa wajen ci gaban al’umma, kuma ayyukansa sun taɓa rayuwar mutane da dama.”
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, da sauran masu ruwa da tsaki a jihar.

By ukarofi