
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Hon. Muhammad Adamu Oyanki ya haɗu iftila’i yayin da wani mummunan hatsarin mota ya rutsa da shi a babban titin Keffi zuwa Akwanga a jihar.
An gano cewa al’amarin, wanda ya faru a jiya Litinin, ya yi sanadin damejin motar ɗan majalisar, wadda daga bisani aka garzaya da ita farfajiyar majalisar da ke Lafiya.
Kakakin majalisar, Hon. Dakta Ɗanladi Jatau da wasu ‘ya’yan majalisar sun je gane wa idonsu halin da motar ke ciki yayin da aka kai ta Lafiya.
Da yake jawabi, Jatau ya bayyana al’amarin a matsayin abin tausayi, inda ya yi godiya ga Allah ganin cewa babu asarar rai a sakamakon faruwarsa.
A cewar jaridar Daily Trust, mataimakin kakakin yana cikin ƙoshin lafiya yayin ake cigaba da kula da lafiyarsa tun bayan faruwar al’amarin.
Ana samun ƙaruwar faruwar hatsari a titinan Nijeriya da dama da ke haddasa rasa rayuka da jikkata, waɗanda wasu masu ruwa da tsaki ke ɗora alhakinsu akan rashin ƙwarewa a tuƙi yayin da wasu ke ganin gazawar gudanarwa ce daga ɓangaren gwamnati.
