Hedikwatar INEC ta ƙi amincewa da bayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Adamawa

*Ta ba da umarnin dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaɓe

Babban Ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ya dakatar ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen cike giɓi na Gwamnan Jihar Adamawa da ya gudana ranar Asabar.

Ofishin ya ɗauki wannan mataki ne bayan da labarin ayyana ‘yar takarar Jam’iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru (Binani) a matsayin wadda ta lashe zaɓe da Kwamishinan Zaɓe na jihar, Farfesa Hudu Yunus Ari, ya yi a ranar Lahadi ya isa gare shi.

Cikin sanarwar da INEC ta wallafa a shafinta na Tiwita mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan hukumar, Barista Festus Okoye, ta ce ba ta yarda da abin da ya faru ba.

“Hankalin hukumar ya kai kan batun ayyana wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Adamawa wanda Kwamishinan Zaɓe na Jihar (REC) ya yi duk da tsarin bai kammala ba.

“Matakin karɓe ikon Baturen Zaɓe da Kwamishinan ya ɗauka ba daidai ba ne, kuma ba shi da wani tasiri.

“Don haka an dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaɓen cike giɓin da ya gudana.

“Da Kwamishinan da Baturen Zaɓe da ma dukkan waɗanda ke da hannu a lamarin ana gayyatar kowa zuwa Hedikwatar Hukumar da ke Abuja nan take,” in ji sanarwa.

Kwamshinan Zaɓe na Jihar Adamwa, Farfesa Hudu Yunus Ari, shi ne ya bayyana nasarar Binani a cibiyar tattara sakamakon zaɓen.

Magoya bayan jam’iyyar PDP sun nuna rashin jin daɗinsu ganin Kwamishinan Zaɓe na jihar ne ya bayyana sakamakon zaɓen maimakon Baturen Zaɓe.