Daga JOHN D. WADA a Lafia
Ɗan takarar kujeral dan majalisar wakilai ta tarayyar ta Obi da Lafiya a jihar Nasarawa Injiniya Akaba Joshua Peter ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar majalisar wakilai ta Lafia/Obi a ƙarƙashin jam’iyyar LP.
Akaba daga Dudu Guru a ƙaramar hukumar Obi ɗan tsohon Rev. Peter G. Akaba ne amintaccen ERCC. Yace ban gaskiya da sha’awar yi wa jama’a hidima ne suka motsa shi ba son kai ba.
Yace mutanen mazaɓar Lafia/Obi musamman Obi ba su ji tasirin gwamnati ba. Yace mazabar ta kunshi ƙabilu daban-daban kamar Mada da Alago da Koro da Kanuri da Gwandara da sauran su don haka ya kamata a yi adalci da daidaito wajen raba muƙamai.
Yace Koro sun dade suna goyon bayan sauran ƙabilu amma ba a rama musu ba. Ya tuna cewa tun 1999 kujerar ta zauna a Lafia. A 1999, Suleiman Yusuf ya yi takara da goyon Obi. A 2003, Danladi Almakura har 2011. A 2011, Obi sun sake goyon Lafia, Dr. Joseph Haruna Ikpe har 2015. Daga baya Hon. Sarki Dahiru ya riƙe ta shekaru 12.
Yace Agwatashi ta samar da Sanata Solomon Adokwe na shekaru 12, yayin da Obi ba ta taɓa samar da ɗan majalisar wakilai ko Sanata ba. Ya ce lokaci ya yi da kujerar za ta koma Obi.
Ya kuma amince ba shi kaɗai ne ɗan takara daga Obi. Akwai Dalla a PDP, Hon. Ogbele a NDC da Dr. Anzaku a NNPP inda ya roƙi Lafia ta yi haƙuri.
Ya soki SDP inda ya ce ‘yan takarar gwamna da Sanata da majalisar wakilai duk daga Lafia ne.
Ya kwatanta Obi da Isra’ilawa a Masar inda yace kamar yadda sunansa Joshua ke nufi zai kai Obi zuwa ƙasar alƙawari.
A kan amincewa da Solomon Aquashiki yace ba shi da matsala da hakan domin masu zaɓe ne za su yanke shawara. Yace wasu suna amfani da kuɗi su sayi amincewa amma shi yana neman muƙami daga Allah ne. Yace babban sarkinsa bai ziyarci Aquashiki don siyasa ba, kuma ƙungiyar matasan Migili ta musanta amincewa da shi.
A kan ajandarsa yace a yanzu ya fitar da shiri mai maki huɗu – noma da ilimi da ƙarfafa matasa da mata da gina kayayyakin more rayuwa.
A noma yace manoma ba za su iya sayen takin zamani da maganin ciyawa ba kuma ya yi alƙawarin mayar da Lafia/Obi daga cinye zuwa samarwa.
A ilimi kuma yace makarantun ƙauyuka sun lalace yara suna zaune a ƙasa a Fadama Bauna da Agwata da Adudu da Ajaragu da Musha da Takalafia.
A matasa da mata yace matasa da yawa sun kammala karatu sun zauna ba aiki har shekaru 15 zuwa 20, wasu sun tafi Benin su yi keke da mashin. Ya yi alƙawarin cibiyar kasuwanci a Agwatu da ƙarfafa mata ta hanyar basu jari.
A kayayyakin more rayuwa, ya ce asibitocin ƙauyuka ba sa aiki, kuma yawancin abin da ake kira gadoji culverts ne da za a iya gina su da Naira miliyan 3.5 zuwa 5, kamar hanyar Kaba Two Men, Kaba Gwede da Kaba Dudu Gurung.
Ya kwatanta takararsa da Dawuda da Goliath yana mai cewa zai kayar da Goliath a 16 ga Janairu mai zuwa wato ranar zaɓen kenan.
