Hukumar ‘Yan sanda ta sanar da fara horar da sabbin jami’ai bayan rikici da rundunar

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar kula da ƴan sanda, PSC ta sanar da lokacin fara horar da sabbin jami’ai bayan sa’insa tsakanin ta da rundunar kan jadawalin waɗanda aka ɗiba.

Yayin da PSC ta fitar da sanarwar ɗaukar sabbin jami’ai 10,000, a ranar 4 ga watan Yuni, rundunar ‘Yan sanda ta ƙi amincewa da hakan, ta na mai cewa akwai rashawa da ƙin bin hanyoyin da su ka dace wajen ɗaukar ma’aikatan a cikin hakan.

Duk da matsayar rundunar, PSC ta ƙi sauya jadawalin wanda hakan ya sa Ministan harkokin Ƴan sanda, Ibrahim Gaidam ya shiga cikin lamarin tare da sulhunta su.

Wata sanarwa da PSC ta fitar a ranar Litinin ta ce, hukumar ɗaukar aikin ɗan sanda ta tabbatar da ranar 10 ga watan Agusta, 2024 a matsayin lokacin fara horar da jami’an da su ka nemi aikin a 2022.

Waɗanda su ka yi nasarar samun aikin za su iya dubawa ta adireshi kamar haka; ‘http://apply.Policerecruitment.gov.ng’ domin tabbatarwa.

By Babaji