Hukumar zaɓen Jihar Kebbi ta yi sabon shugaban riƙon ƙwarya

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Ranar 18 ga wannan watan na Satumba, 2026 Sabon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kebbi na riƙon ƙwarya kwarya Alhaji Muhammad Kaura Dan Hakimi Zagga ya karɓi ragamar jagorancin hukumar daga hannun Honarabul Aliyu Muhammed Mera.
Da ya ke jawabi a wajen bikin barin ofis ɗin, Honarabul Aliyu Muhammed Mera mai barin gado ya bayyana cewa a tsawon zaman sa a wannan ma’aikata tun daga 2017, 2019, 2022 har zuwa 2024 an sami nasarorin aiwatar da ayyukan da aka ɗora mata tun kama daga samar da tsare-tsare na gudanarwa ilmantar da al’umma kan harkokin da suka shafi zaɓe har zuwa shirya zaɓukan ƙananan hukumomi.

Ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Kebbi bisa ga damar da ya ba shi na jagorancin hukumar na tsawon lokaci inda ya kuma ya ja hankalin sabon shugaban da ya gudanar da ayyukan sa bisa ga tsari tare da bai wa dukkan ma’aikatan sa haƙƙoƙin su a wajen aiki wanda shi ne zai sa su yi aiki ba tare da jan ƙafa ba domin cimma nasara.

A na sa jawabi, sabon shugaban riƙon ƙwarya Alhaji Muhammad Kaura Dan Hakimi Zagga ya yaba wa Alhaji Aliyu Mera bisa ga gudummawar da ya bayar a lokacin sa.
Ya kuma bayar da tabbacin aiwatar da ayyuka bisa ga doka ba tare da nuna wani bambanci ko son kai ba, tare da kira ga jam’iyyun siyasa da jami’an tsaro, ƙungiyoyi masu zaman kan su da sauran al’umma da su bai wa hukumar haɗin kai musamman wajen aiwatar da zaɓukan ƙananan hukumomi a cikin lumana.

By ukarofi

Leave a Reply