Ibok-Ete Ibas ya kama aiki a matsayin jagora a Ribas

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin Admiral (VA) na Sojojin ruwa ta Nijeriya (mai ritaya), Ibok-Ete Ibas, ya kama ragamar jagorancin Jihar Ribas, wato ‘Rivers Administrator’, biyo bayan naɗa shi da Shugaba Bola Tinubu ya yi a ranar Talata sakamakon sanya dokar ta-ɓaci a jihar.

Shugaba Tinubu ya yi hakan ne a yayin da ayyukan lalata layukan mai ya yawaita, wanda Gwamna Siminalayi Fubara da aka dakatar ya gagara neman sa a kai.

An dakatar da Gwamna Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu da dukkan zaɓaɓɓun mambobin Majalisar Dokoki ta jihar na tsawon watanni shida.

A sanarwar da Shugaba Tinubu ya yi, wanda PRNigeria ta ruwaito, naɗa Ibas bai shafi harkokin shari’a a jihar ba, inda za a cigaba da gudanar da su kamar yadda aka saba.

Haka kuma ba zai kafa wa sabuwar doka ba, saidai zai riƙa gudanar da aikinsa bisa yadda hali ya bada dama da kuma neman amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Ana ganin wannan hukunci da Shugaba Tinubu ya yi zai taimaka wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa da warware matsalolin rikicin siyasa a jihar.