Daga USMAN KAROFI
Hukumar ICPC ta shigar da sabbin tuhume-tuhume na laifi a kan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, tare da wasu mutum bakwai bisa zargin almundahana da wanke kuɗaɗe da suka shafi aikin CCTV na tsaro na naira biliyan 10.8 a jihar. A cewar takardun kotu da aka shigar a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar 17 ga Afrilu, hukumar ta gabatar da tuhume-tuhume guda 11 ƙarƙashin dokar hana wanke kuɗaɗe ta shekarar 2022.
Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kaduna kuma shugaban Liberty Television, Alhaji Tijjani Ramalan, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa El-Rufai da sauran wadanda ake tuhuma za su gurfana a gaban kotu nan ba da jimawa ba. ICPC ta zargi El-Rufai da amincewa da bayar da kwangilar CCTV ta naira biliyan 8.68 a watan Disambar 2015 ga wani kamfani da ake zargin bai da ƙwarewar gudanar da aikin.
Haka kuma, hukumar ta ce an samu karbar kuɗaɗe masu yawa da kuma canja wurinsu tsakanin shekarun 2017 zuwa 2022 ta hannun wasu mutane da kamfanoni da ke da alaƙa da aikin CCTV, ciki har da Singularity Network Security Limited da wasu kamfanoni. Daga cikin waɗanda aka ambata akwai tsohon jami’in gwamnatin Kaduna Jimi Lawal, manyan jami’an IHS Towers, da kuma kamfanoni biyar. An kuma ambaci Bashir El-Rufai, ɗaya daga cikin ‘ya’yan El-Rufai, amma ba a sanya shi cikin waɗanda ake ƙara ba. Wannan shi ne karo na uku da ICPC ke shigar da ƙara a kan tsohon gwamnan tun daga watan Maris, yayin da shi kuma ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa a gaban kotu.
