Daga ALI ABUBAKAR SADIK
Wato ina wani shafi da turawa da yan hindu ke da yawa sai naga wani ya yi posting wani labari don a yi dariya tare da ci wa Musulmi mutunci… ga labarin…
“Wai wani Musulmi ne a kasar Ingila ya shiga Tasi za a kaishi unguwa. Su na fara tafiya sai direban ya kunna kida. Karaf sai shi wannan Musulmi ya ce “Malam kashe kidan nan saboda musulunci ya haramta kida kuma annabi bai yi ba.”
Sai dan Tasi ya kashe kidan sannan ya nemi waje ya yi parking ya tsaya sannan ya juyo kan mutumin ya ce masa “Me gida sai ka sauka ko? Idan ya so, sai ka jira Rakumi ya zo ka hau tunda dai annabin bai hau mota ba sai rakumi.”
To wannan ba shine babban takaicin ba. Daruruwan mutane su ka yi caa kan wannan labari ba abinda a ke yi sai zagin Musulmi da Musulunci ana mana shagube iri-iri.
Me ya jawo mana haka?
Mun yi watsi da ilimi mun rungumi karamin-sani. Mun yi watsi da wayewa mun rungumi gidadanci. Mun yi watsi da kimiyya mun rungumi tsatsuniyoyi. Mun yi watsi da umarnin Allah cikin ƙurani mun rungumi fatawar malamai.
Mun manta da tarihinmu na baya yadda musulmi ne suka gina ginshikin ilimin kwamfuta da lissafi,, na kere-kere da magunguna.
Dole idan muna son mu dawo da martabarmu mu bi umarnin farko kuma mafi girma da Allah ya saukar na cewa “Yi karatu” sannan mu kwaikwayi adalci irin wanda Manzo ya shimfida a Madina.
Allah ya ba mu iko.
Sadiƙ mai lura da al’amuran yau da kullum ne a Kano
