Imagireshin za su fara bai wa ’yan Nijeriya mazauna waje fasfon gaggawa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ta bayyana cewa za ta ƙaddamar da sabon fasfon gaggawa na tafiya ɗaya ‘Single Travel Emergency Passport’ (STEP), domin tallafa wa ’yan Nujeriya da ke ƙasashen waje waɗanda fasfo ɗinsu ya ƙare, ya ɓace, ko kuma aka sace musu, domin su samu damar dawowa gida cikin sahihanci da tsaro.

Wannan mataki, wanda zai maye gurbin ‘Emergency Travel Certificate’ (ETC) da ake amfani da shi yanzu, na cikin shirin sabunta harkokin shige da fice da inganta tsaro da tabbatar da sahihin fasfo ga ’yan Nijeriya, bisa tsarin duniya.

Hedikwatar hukumar ta bayyana hakan a taron haɗin gwiwa na ƙasashen Afirka da Turai kan batutuwan ƙaura, da aka gudanar a Abuja tare da wakilan ƙungiyoyi kamar ECOWAS, AU, EU, NAPTIP, da sauran hukumomin kula da shige da fice da tsaro.

A cewar Babbar Konturolar Shige da Fice, Kemi Nanna Nandap, STEP za a riƙa bayar da shi a ofisoshin jakadanci da ofisoshin diflomasiyyar Nijeriya a ƙasashen wajen. Za a yi amfani da shi sau ɗaya ne kawai, kuma daga ƙasar waje zuwa Nijeriya kaɗai.

Ta ce wannan tsari zai taimaka wajen: kare bayanan shaidar jama’a, tabbatar da tsaro da tantance sahihin ɗan ƙasa, sauƙaƙa wa masu shiga mawuyacin hali samun taimako cikin gaggawa da bunƙasa sahihan bayanai na shige da fice kamar yadda duniya ke bi.

Nandap ta jaddada cewa NIS na ci gaba da aiwatar da gyare-gyare na zamani, ciki har da horar da ma’aikata da inganta mu’amala da sauran ƙasashe, domin tabbatar da shige da fice na gari, tsaro, da bin ƙa’idojin duniya.

Ta kuma nanata cewa gwamnatin Nijeriya na ƙarfafa haɗin kai wajen yaƙi da fataucin mutane da safarar baƙin haure, tare da mayar da hankali kan kare waɗanda ke cikin hali, da hukunta masu aikata laifin.

“Za mu ci gaba da bin ƙa’idojin duniya wajen kare martabar Nujeriya da tabbatar da tafiyar da batutuwan ƙaura cikin tsari,” inji ta.

Sabon takardar na zuwa a daidai lokacin da hukumomi ke ƙara ƙaimi wajen gyara fannin shige da fice da sauƙaƙa hanyoyin samun takardun tafiye-tafiye ga ’yan ƙasa.

By ukarofi