Daga MAHDI MUSA MUAHMMAD
Sojojin Nijeriya tare da haɗin gwiwar dakarun Nijar sun cimma gagarumar nasara a safiyar Talata, bayan sun fatattaki mummunan harin da Boko Haram ta kai a Malam Fatori, hedikwatar ƙaramar hukumar Abadam a jihar Borno.
Aƙalla ‘yan ta’adda shida aka kashe a wurin, yayin da sauran suka tsere da munanan raunuka bayan artabu mai tsanani.
Rahotanni daga hukumomin tsaro sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 4:30 na safe, inda suka yi ƙoƙarin mamaye sansanin Forward Operating Base (FOB) na sojoji.
Boko Haram ta yi amfani da manyan makamai, har da makaman mota, mortars, da kuma bindigogin diron ɗin da aka ɗora bama-bamai a kansu, a cikin shirin karya shingayen tsaron sojoji.
Wani babban jami’in soja ya bayyana cewa maharan sun fito ne daga ɓangarori daban–daban na yankin Tumbuns, suna harba mortar da aika diron ɗin bama-bamai kan sansanin, amma dakarun Nijeriya sun daƙile su cikin ƙwarewa, musamman bayan samun taimakon jiragen yaƙin sojojin Nijar.
Duk da raunukan da wasu sojoji da ‘yan CJTF suka samu, rundunar Operation Hadin Kai ta kaddamar da farmaki mai ƙarfi tare da ƙarin jami’ai daga Sector 3, wanda hakan ya tilasta wa maharan ja da baya cikin kangaren Kogin Chadi.
Wani rahoto ya nuna cewa jama’a da dama daga cikin ‘yan ta’addan sun mutu a hare–haren sama da sojojin Nijeriya da Nijar suka aaddamar yayin bin sawun da suka tsere.
Mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai, Lt. Col. Sani Uba, ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce dukkan sojojin da suka ji rauni sun samu kulawar gaggawa kuma suna cikin aoshin lafiya.
Ya jaddada muhimmiyar rawar da bayanan leƙen asiri (ISR) na MNJTF suka taka wajen bin diddigin ‘yan ta’addan da hana su sake taruwa.
“Dakarunmu suna cikin ƙwarin gwiwa, suna ci gaba da mamaye fagen daga da kare yankin,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, Babban Hafsin Sojoji ya yaba da jarumtar sojojin da tsayuwa tsayin daka wajen kare ƙasa da tabbatar da zaman lafiya.
