Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta musanta zargin da ake yaɗawa cewa ana tilasta jami’an ta a faɗin Nujeriya su sayi wani littafi mai suna “Attitudinal Change Handbook for the Nigeria Police Force” akan kuɗin Naira 2,000.
Wani rahoto daga wata jarida ta yanar gizo ya yi iƙirarin cewa an bayar da umarnin wajabta sayen littafin tare da sanya wa’adin kammala karanta wa da yiwuwar ladabtar da duk jami’in da ya ƙi bi.
Sai dai bayanan da aka samu a ranar Litinin sun nuna cewa izinin da Hedikwatar ‘Yan Sanda ta bayar shi ne bai wa marubucin littafin, Dr. Joseph Danley, damar tallata littafin ga jami’an da suke sha’awar saya da raɗin kansu.
Wannan izini, wanda aka rubuta ranar 28 ga Mayu, 2025, tare da sa hannun Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da horo, Rashid Afegbua, a madadin DIG na Horo, ya gabatar da marubucin zuwa sassan rundunar a faɗin ƙasa domin tallata littafin ga masu buƙata.
A cikin wasiƙar an ce: “An umurce ni na gabatar da Dr. Joseph Danley, marubucin littafin ‘Attitudinal Change for Nigeria Police Force’, tare da isar da amincewar IGP domin ba shi damar tallata littafin ga jami’an da ke son saya.”
Da yake magana da manema labarai, Kakakin ‘Yan Sanda na kasa, ACP Benjamin Hundeyin, ya yi watsi da rahotannin da ke zargin tilastawa, yana cewa labaran ba su da tushe.
Ya ce babu wani umarni da ke tilasta jami’ai su saya. “Na bincika kuma babu wata hedikwata ko kwamanda da ta tilasta sayen littafin. An bayyana a rubuce cewa siyan littafin na son rai ne,” inji shi.
Hundeyin ya ƙalubalanci duk wani jami’in da aka tilasta wa ya mika ƙorafi ta hanya ta doka, maimakon yada bayanan da ba a tabbatar da su ba cikin kafafen yada labarai. Ya ce Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) na da hurumin ladabtar da duk masu aikata irin wannan matsala.
A nasa ɓangaren, marubucin littafin, Dr. Danley, ya ce an kirkiro wannan shiri ne domin ƙarfafa ɗabi’un aiki da sake gina tunanin ingantaccen aiki a hukumar ‘Yan Sanda. Ya bayyana cewa asalin kuɗin horon da ya shafi littafin shi ne N25,000 amma IGP Kayode Egbetokun ya bada umarnin a cire kuɗin, a bar horon kyauta, sai duk wanda ya ga dama ya saya littafin.
Ya ce, an riga an kai littattafai ga wasu sassa inda jami’an da suka ga dama suka saya ba tare da wani tilas ba.
Wannan ƙarin bayani ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen jama’a kan raɗe-raɗin da suka shafi tilastawa jami’ai ɗaukar nauyin wasu abubuwa a rundunar, lamarin da ke ta ƙara fusata al’umma kan yadda ake gudanar da al’amura a wasu ɓangarorin hukumar.
Rundunar ta ƙara jaddada cewa duk wani tabbacin tilastawa za a magance shi nan take tare da tabbatar da bin ƙa’ida, adalci da gaskiya a ci gaba da gyaran tsarin ta.
