Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Matuƙan Jiragen Sama da Injiniyoyin Kayan Jirage ta Nijeriya (NAAPE) ta sanar da ƙaddamar da sabon tsarin inshorar “Loss of Licence”, domin tabbatar da kariya ga mambobinta — musamman matuƙa da injiniyoyi — idan suka rasa lasisin aikinsu sakamakon rashin lafiya ko wasu dalilai na ƙwarewa da ƙa’ida da ka iya hana su ci gaba da aiki.
A cewar ƙungiyar, wannan shiri da aka ƙirƙira tare da First Standard Insurance Brokers, zai ba da cikakkiyar kariya ta inshora ga duk matuaa jirage da injiniyoyin jirage a Nijeriya da suka fuskanci rasa lasisin aikinsu saboda nakasar jiki, matsalar lafiya ko wani yanayi da ya hana su ci gaba da gudanar da aikinsu yadda ya dace.
Shugaban NAAPE, Kyaftin Bunmi Gindeh, ya bayyana cewa manufar ita ce kare rayuwar waɗanda suka sadaukar da basira, lokaci da lafiyarsu wajen tabbatar da amincin tashi da saukar jirage a Nijeriya. Ya ce tsarin zai biya diyya ga waɗanda abin ya shafa, bisa sharuɗɗan da aka gindaya, domin tallafa musu wajen farfaɗo da rayuwa ko kuma shawo kan matsalar lafiyar da ta hana su aiki, ba tare da shiga cikin matsananciyar ƙuncin kuɗi ba.
“Mun ga yadda wasu daga cikin abokan aikimu ke fuskantar matsananciyar wahala bayan rasa lasisin aiki sakamakon yanayin lafiya da ba a zata ba. Wannan shiri tamkar kariya ce ga su. Zai tabbatar da cewa ba wanda zai zauna cikin wahala shi kaɗai idan haka ta faru. Duk ɗan aikin jirgin sama ya cancanci wannan kariyar,” inji Mataimakin Shugaban ƙungiyar, Injiniya Mudi Muhammad.
Gindeh ya ce ƙungiyar ta cimma wannan mataki ne bayan shawarwari masu zurfi da masana da manyan jami’an fannin jiragen sama, domin tabbatar da cewa an samar da kariyar rayuwa da ta dace ga waɗanda ke cikin sahun gaba wajen tabbatar da tsaron fasinjoji da jirage.
Ya aara da cewa, NAAPE na kallon wannan mataki a matsayin babbar nasara ga ma’aikatan jirgin sama, kuma alama ce ta himma wajen samar da zaman lafiyan aiki da dorewar sana’a a fannin su, musamman a wani lokaci da fannin su ke buƙatar ƙarin kwarin gwiwa da kariya.
Wannan mataki, a cewar ƙungiyar, zai iya buɗe ƙofa ga ƙarin manufofi masu ƙarfafa gwiwa da kare martabar ma’aikatan jirgin sama a Nijeriya.
