
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) ya gargaɗi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu akan shirinta na karɓar bashin Dala biliyan 5 daga Bankin First Abu Dhabi (UAE) ta hanyar tsarin Total Return Swap.
Wakilin IMF na Nijeriya, Christian Ebeke, ya bayyana cewa wannan yarjejeniya tana da rufa-rufa da rikitarwa, tare da yiwuwar haɗarin ƙarin biyan kuɗi (margin calls) da kuma rashin tabbas akan tsawon lokaci.
Gwamnatin na shirin amfani da kuɗin ne wajen sake fasalin bashi masu tsada da kuma ayyukan more rayuwa, tare da amfani da takardun Naira a matsayin jingina.
Saidai IMF ta ba da shawarar Nijeriya ta fi karkata zuwa hanyoyin bashi masu sauƙi da bayyane kamar Eurobonds ko lamuni masu rangwame (concessional loans).
Wannan gargaɗi na zuwa ne a daidai lokacin da bashin Nijeriya ke cigaba da ƙaruwa, yayin da talauci da wahalar rayuwa ke cigaba da shafar miliyoyin ‘yan ƙasa, lamarin da aka ɗauki tsawon lokaci ana fatan shawo kansa.
A cewar Shugaba Tinubu, za a yi amfani da bashin ne wajen aiwatar da kasafi, cigaba da fifita ayyukan ababen more rayuwa da kuma biyan manyan basussukan cikin gida da na ƙasashen waje.
