IPOB, Boko Haram da ISWAP dangin juna ne – Soyinka

Daga AISHA ASAS

Fitaccen marubucin nan Farfesa Wole Soyinka, ya bayya IPOB a matsayin ƙani ga Boko Haram.

Soyinka ya bayyana haka ne duba da irin ɓarnar da ‘yan IPOB ke yi ƙasa musamman ma a yankin Kudu-maso-gabas inda suke karkashe mutane da jami’an tsaro da lalata ofisoshin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da sauransu.

Da yake tsokaci kan batun haramta Tiwita a Nijeriya, Farfesan ya ce gwagwarmayar tsagerun IPOB ba halastacciya ba ce.

Ya ce, “Ba na goyon bayan waɗanda suka ɓuge da ƙona ofisoshin ‘yan sanda tare halaka jami’ansu, lalata ofisoshin zaɓe, yi wa ‘yan siyasa kisan gilla duk da zummar cimma manufofi na siyasa.”

Ya ci gaba da cewa waɗannan maɓarnata dangi ne na Boko Haram da ISWAP da Da’esh da sauransu, waɗanda bai kamata a yi kuskuren ɗaukar su a matsayin masu neman halaliya ba.

A cewarsa a tarihin zaɓuɓɓuka duk duniya, akan yi allawadai, ko ƙaurace ma zaɓe da makamantan haka ba tare da ɗaukar matakin kashe-kashen mutane da lalata dukiyoyin hukuma da na ɗaiɗaikun mutane ba.