Iran ta harba makamai a Gabas ta Tsakiya yayin da Trump ya yi barazanar babbake masarrafar manta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iran ta kai sababbin hare-hare a yankin Gabas ta Tsakiya a yau Talata yayin da babban birninta ya fuskanci farmaki bayan Shugaba Donald Trump ya yi barazanar babbake masarrafar manta.

Fraministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, wanda abokin Trump ne a kai wa Iran hare-hare, ya ce ya cimma sama da rabi na buƙatun sojin ƙasarsa duk da cewa kawo yanzu shugabannin biyu ba su cimma matsayar lokacin da za a kawo ƙarshen yaƙin wanda aka shafe sama da wata guda ana fafatawa ba.

A wani labarin kuma, Donald Trump ya bayyana cewa ƙasarsa na iya ɗaukar matakin ƙwace albarkatun man fetur na Iran musamman a yankin Kharg Island, wato cibiyar da ta fi muhimmanci wajen fitar da man ƙasar.

Trump ya ce, idan rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin Amurka, Iran da Isra’ila bai lafa ba, Amurka za ta iya ɗaukar matakin da ya haɗa da karɓe iko da hanyoyin man fetur na Iran.

Ya kuma kwatanta wannan da irin tasirin da Amurka ke da shi a harkar man ƙasar Venezuela.

Rahotanni sun nuna cewa Kharg Island na da matuƙar muhimmanci ga tattalin arziƙin Iran, domin mafi yawan man da ƙasar ke fitarwa daga nan yake wucewa.

Ana fargabar cewa yunƙurin ƙwace cibiyoyin man Iran ka iya janyo martani mai tsanani daga Tehran, wanda zai ƙara dagula zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

By Babaji