Iraniyawa na jimamin kisan Khamenei yayin da aka fara zanga-zangar adawa da yaƙi a Amurka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dubban Iraniyawa ne suka taru a Birnin Tehran a jiya Lahadi domin nuna jimaminsu na rashin Jagoran Musuluncin ƙasar, Ali Khamenei, wanda hare-haren Amurka da Isra’ila suka yi sanadiyyar mutuwarsa.

An ga yadda dandazon al’umma suka taru a farfajiyar Enghelab Square sanye da baƙaƙen kaya tare da ɗaga tutocin ƙasar da nuna hotunan marigayin.

Hukumomin ƙasar sun tabbatar da rasuwar jagoran mai shekaru 86 ne a safiyar ranar Lahadi bayan sa’o’i ana yaɗa labarin a kafafen sada zumunta.

Tuni dai jama’a da dama suka shiga zanga-zangar adawa da yaƙin a birane da dama na Amurka yayin da masu tsokaci suka yi ta sukar hukuncin Shugaba Donald Trump na ɗaukar matakin soja akan Iran ba tare da amincewar majalisar dokokin Amurka ba.

An ruwaito cewa an yi zanga-zangar a biranen Washington D.C. da New York inda aka ga Mayor Zoran Mamdani ya shiga sahun masu adawa da yaƙin.

A nasa ɓangaren, Donal Trump ya kare hare-haren da cewa Iran ta samar da barazana mai girma ga buƙatun Amurka, matakin da ‘yan Jam’iyyar Republican na majalisar dokokin ƙasar suka goyi baya

By Babaji