Arewa na fuskantar ƙalubalen karatu, musamman ta fuskar tsaro – Jamila Mu’azu Abubakar 

Spread the love

“Babban ƙalubalen dake akwai dama bai wuce salon da ake amfani da shi wajen koyarwa ba”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

(Ci gaba daga makon jiya)

Jajirtattun mata masu ƙwazo da himma kan duk abin da suka sa a gaba, su ne ake kira da Kallabi Tsakanin Rawwuna. Ba domin komai ba kuwa, sai don ƙoƙarin su da rawar ganin da suke takawa, wanda ko a cikin maza ma sai an tona kafin a dace da mai jarumtarsu. Hajiya Jamila Mu’azu Abubakar ɗaya ce daga cikin irin waɗannan matan da ake yi wa laƙabi da Giwar Mata. ƙwararriya ce kuma jajirtacciya kan fagen da aka fi saninta akai, wato fagen ilimi, inda take da gogewa akan ilimantar da ƙananan yara, da waɗanda suke samun rauni wajen fahimtar karatu. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya samu ganawa da ita a ofishin ta dake Jos, inda suka tattauna kan rayuwarta da gudunmawarta a ɓangaren inganta dabarun koyarwa, da ma ƙalubalen da harkar koyarwa ke fuskanta a Nijeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance. 

MANHAJA: A matsayinki ta malama kuma mai kishin ilimi, yaya kike kallon ƙalubalen da harkar ilimi ke fuskanta a arewacin ƙasar nan?

HAJIYA JAMILA: Zahiri Arewa na fuskantar ƙalubale babba, musamman duba da irin yadda matsalar tsaro take shafar harkokin karatu. Yadda ‘yan ta’adda ke yawan kai hare-hare makarantun kwana na ‘yan mata da manyan makarantun ilimi a sassan arewacin ƙasar nan, babban abin tsoro ne da tashin hankali. 

Na ji ɗazu kin ambaci wata ƙungiyar ku ta Arewa Early Readers wanne ayyuka ku ke yi a ƙarƙashin ta? 

Ita wannan ƙungiya haɗaka ce ta ƙawaye da ƴan’uwa masu kishin koyarwa da ilimi kan dabarun inganta ilimantar da ƙananan yara. A ƙarƙashinta ne muka fitar da wasu ƙananan littattafai da aka yi su cikin harshen Turanci da Hausa ta yadda yara za su tashi da sanin ma’anonin kalmomi cikin harshen uwa, kamar yadda yake a baya a tsohuwar dokar koyar da ilimin ƙananan yara a matakin farko, wanda hatta iyaye a cikin gida za su iya amfani da su suna koyawa yaransu a lokacin hutu. Kuma an yi musu bugu mai kyau, ana kuma sayar da su a farashi mai sauƙi. 

A cikin waɗannan littattafai da ku ka buga na ga har da wani da aka ce an sadaukar da shi ne ga fitacciyar ‘yar kasuwar nan, Hajiya Laila Othman, ko me ya ja hankalinku gareta?

Mun yi la’akari ne da irin kyawawan ayyukan da wannan baiwar Allah take yi wajen kula da marayu da ƙananan yara marasa gata. Alal haƙiƙa ita ma kanta Hajiya Laila Othman ba ta san da aikin da muka yi ba. Mun yi wannan abin ne lura da kasancewar ita ‘yar Arewa ce kuma musulma, mai taimakon jama’a. Ta kasance abin koyi ga mutane da dama, sakamakon abubuwan da take yi na tausayawa na ƙasa da ita. Muna ganin halayen da take nunawa da tallafin da take bayarwa, wasu abubuwa ne na tarbiyya da take ɗora yara akai don su zama shugabanni nagari, bayan sun girma. Gaskiya Laila Othman tana bai wa al’umma gudunmawa sosai. 

Wacce shawara za ki bai wa gwamnati da masu ruwa da tsaki kan samar da dabarun inganta koyarwa?

Babban ƙalubalen dake akwai dama bai wuce salon da ake amfani da shi wajen koyarwa ba. Idan gwamnati za ta ba da muhimmanci wajen horar da malamai sanin dabaru da hikimomin koyar da ƙananan yara a matakin farko babu shakka za a samu canji a tsarin yadda ake koyarwa yara ilimi. Domin an ce ingancin ilimi ba zai wuce ingancin malamai ba. Gwargwadon ƙwarewar malami, gwargwadon tasirin da koyarwarsa za ta yi akan ɗalibansa.

Sannan abu na biyu, kirana ga masu ruwa da tsaki a harkar ilimi, a tashi tsaye domin ceton harkar koyarwa a ƙasar nan. Idan ka lura duk yaron da aka lura bashi da ƙoƙari sosai, sai a ce ya je ya karanta aikin koyarwa. Ko idan mutum ya rasa aiki, sai a ce ko da koyarwa ne ya shiga mana. An zubar wa ilimi darajar da yake da ita, mutane ba sa ganin harkar koyarwa a matsayin wani aiki mai buƙatar ilimi da gogewa ba. Babu yadda za a yi wanda ba shi da ilimi ya koyawa mai neman ilimi. Ina mai ba da shawara ko a jami’a mutum yake so ya nemi damar shiga sashin koyarwa, a tsaurara ƙa’idojin shigar ta yadda zai yi gogayya da sauran manyan darussa irin su koyon aikin likita da lauya da injiniyanci. Idan ba a ɗauki matakan inganta albashin malamai, samar da hararwa akai-akai, da darajanta harkar koyarwa ba to, za a daɗe ana wahala akan ilimi.

Ban da zaman makaranta da koyarwa, wanne abu ki ka fi jin daɗin yi?

To, a gaskiya babu abin da nake son yi idan na keɓe ba na komai na makaranta,  nakan shagaltu ne da ambaton Allah, ina azkar, ko kuma yin wani abu na alheri da Allah zai yi farinciki da shi.

Me ki ke so yaranki, musamman mata, suna koya daga rayuwarki?

Ina son su koyi ƙwazo da jajircewata, da kuma dogaro da kai. Bisa la’akari da yadda rayuwar aure ta zama yanzu, ba wuya ka ga yarinyar mace ta zama abin tausayi ta lalace, saboda rashin abin yi.

Wacce karin magana ce ta fi tasiri a rayuwarki?

Babu maraya sai rago.

Masha Allah. Na gode.

Ni ma ina godiya ƙwarai da gaske.

By ukarofi