Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Alhaji Tukur Hassan Ɗan-Ali ya miƙa ragamar ci gaba da shugabantar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Katsina ga Mataimakinsa, Comrade Ismail Adamu, domin jagorantar ƙungiyar a matsayin riƙon ƙwarya.
Ɗan-Ali ya miƙa ragamar ne bisa tanadin dokokin ƙungiyar, sakamakon kammala aikinsa na gwamnati da ya yi lamarin da ya wajabta masa sauka daga muƙamin shugabancin ƙungiyar (NUJ) reshen jihar.
A nasa jawabin Alhaji Tukur Hassan Ɗan-Ali wanda a halin yanzu ya sami muƙamin babban sakatare a ma’aikatar haɗa labarai ya bayyana godiya ta musamman ga duka mambobin ƙungiyar bisa cikakken goyon bayan da suka ba shi a tsawon lokacin da yake shugabanci. Ya ce haɗin kai, fahimta da jajircewar ‘yan jarida ne suka taimaka wajen cimma nasarorin da ƙungiyar ta samu a lokacinsa.
Tsohon shugaban ya yabawa gwamnan Jihar Katsina bisa gagarumin ƙoƙari da yake yi wajen tallafa wa harkokin ‘yan jarida, inda ya bayyana cewa irin wannan tallafi na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa aikin jarida da kare martabar masu aikin yaɗa labarai a jihar.
A nasa ɓangaren, sabon shugaban riƙon , Kwamared Ismail Adamu ya nuna matukar jin daɗin sa da amincewar da aka ba shi na jagorantar ƙungiyar a wannan muhimmin lokaci inda ya bayyana cewa zai yi iya ƙoƙarin sa wajen ci gaba da tafiyar da harkokin ƙungiyar bisa gaskiya adalci da bin doka tare da tabbatar da haɗin kai tsakanin mambobin NUJ kafin gudanar da zaɓe.
Kwamared Ismail Adamu ya kuma yi fatan alheri ga tsohon shugaban ƙungiyar, inda ya yaba wa jajircewa da kyakkyawan shugabanci da Alhaji Tukur Hassan Ɗan-Ali ya nuna a lokacin mulkinsa wanda yasa hakan Gwamna Dikko Raɗɗa ya ga cancantar har ya bashi muƙamin babban sakatare.
Kwamred Ismail yayi alƙawarin gina nasarorin da aka samar a baya domin ci gaban ƙungiyar da kare muradun yan jarida a Jihar Katsina.
Bikin miƙa ragamar mulkin ya gudana ne a sakatariyar ƙungiyar da ke Katsina.
