Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan ya amince da samar da babura masu amfani da lantarki ga malaman makaranta na karkara.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya sanar da haka a lokacin da ya halarci bikin ranar Malaman Makaranta ta Duniya na shekarar 2026, inda gwamnatin jihar ta raba babura ga malaman da suka fi hazaƙa wajen aiki.
Gwamnati kuma ta raba kayan koyo da koyarwa, da kuma kayan aiki na ɗakin gwaje-gwaje (Lab) ga wasu makarantun sakandare domin inganta harkar ilimi.
Gwamnatin jihar ta karrama jajirtattun malamai da shugabannin makarantun sakandare (Principals) da suka nuna ƙwazo da jajircewa wajen aikinsu.
Malam Dikko Raɗɗa, ya ce bikin ranar Malaman Makaranta ta Duniya wata dama ce ta musamman da ke ba gwamnati damar yaba wa rawar da malamai ke takawa wajen gina al’umma da tabbatar da kyakkyawar makomar jihar Katsina.
Ya jaddada cewa ilimi shi ne ginshiƙin mulkinsa, inda ya bayyana cewa ba za a samu cigaba mai ɗorewa ba sai an samar da ingantaccen tsarin ilimi tare da malamai masu ƙwarewa, jajircewa da kuma ƙwazo.
Da yake bayyana irin gudummuwar da gwamnatin shi ta bada a fannin ilimi ,inda ya bayyana cewa gwamnatin sa ta ɗauki sama da malamai 7,000 a aikin koyarwa domin magance ƙarancin malamai a makarantun firamare da sakandare, kuma ana shirin ɗaukar ƙarin malamai a wannan shekara domin ƙara inganta tsarin ilimi.
Haka kuma, ya bayyana cewa a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, gwamnati ta ware kaso mai tsoka ga ɓangaren ilimi, domin inganta gine-ginen makarantu, walwalar malamai, samar da kayan koyo da koyarwa, da ƙara inganta tsarin koyarwa.
Gwamnan ya sanar da amincewar gina sabbin makarantun sakandare 70 a faɗin jihar, tare da gyaran manyan makarantu da samar da kayayyakin koyarwa.
“Haka kuma, gwamnatin ta amince da kafa cibiyoyin horas da nalamai a kowacce shiyya ta jihar guda uku domin horaswa, da ƙara ƙwarewar malamai,” Dikko ya sanar da haka.
Gwamna Raɗɗa ya tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta gabatar da alawus-alawus na ƙarfafa gwiwar malamai na karkara, tare da samar masu da babura masu amfani da wutar lantarki (electric motorcycles) domin rage wahalhalun sufuri da ƙara inganta aikin koyarwa a yankunan da ke da nisa.
Ya yaba wa malamai da ɗaliban da aka karrama a yayin bikin, tare da ƙarfafa su da su ci gaba da jajircewa da sadaukarwa.
Tun da fari Kwamishinan Ilimin firamare da sakandare na Jihar Katsina Hon. Yusuf Sulaiman Jibia, ya bayyana cewa bikin wata babbar dama ce ta nuna godiya ga malamai, tare da jaddada cewa gwamnatin Dikko Raɗɗa ta ɗauki ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban jihar.
Shi ma, shugaban hukumar Ilimin vai ɗaya ta Jihar Katsina (SUBEB), Dakta Kabir Magaji, ya bayyana cewa hukumar na ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren da za su inganta harkar koyarwa da walwalar malamai a faɗin jihar.
A nasa ɓangaren, shugaban hukumar kula da malaman makaranta (Teachers Service Board), Sada Ibrahim, ya yaba da irin kulawar da gwamnatin jihar ke bai wa malamai, yana mai cewa hakan zai ƙara musu ƙwazo da ƙwarin gwiwa wajen gudanar da aiki.
A jawabin godiya a madadin ƙungiyar iyayen yara ta jiha (PTA) Ƴan ɗakan Katsina Hakimin Dutsin-ma Alh. Sada Muhammad Sada, ya yaba da tsare-tsaren gwamnatin jihar na bunƙasa harkar ilimi da walwalar malamai da ɗalibai.
Taron ya samu halartar shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, sakataren gwamnan Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, Shugaban ma’aikatan gwamnatin Alh. Falalu Bawale, ‘yan majalissar zartaswa, da sauran jami’an gwamnati.
