Jagora a JIBWIS, Sheikh Saed Hassan Jingir, ya kwanta dama

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Allah Ya yi wa babban malamin addinin Musulunci a Nijeriya, Sheikh Sa’idu Hassan Jingir rasuwa, bayan fama da rashin lafiya.

Marigayi Sheikh Sa’idu Hassan Jingir shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na II na ƙasa na ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iƙamatis Sunnah (JIBWIS).

Sakataren Yaɗa Labarai na JIBWIS, Hon Ahmad Ashiru, ya tabbatar da rasuwar sa ga jaridar Blueprint ranar Alhamis, a Jos, babban birnin jihar Filato.

Ya ce, “Innalillahi Wa’inna Illaihi Rajiun, na tabbatar da rasuwar Sheikh Saeed Hassan Jingir, wanda ya rasu a ranar Alhamis a gidansa.

A cewar Ahmad Ashiru, Sheikh Jingir ya daɗe yana fama da rashin lafiya, kuma “Yau Allah ya kawo ƙarshen cutar.

Ya ce, marigayi Jingir ya rayu sama da shekaru 70, ya bar mata da yara sama da 40.

Dubban al’ummar Musulmi ne suka halarci jana’izar Sheikh Hassan Jingir, a garin Jos.

An gudanar da sallar jana’izar ne a ranar Alhamis a unguwar Anguwan Rimi da ke ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.

By ukarofi