Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jigon Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya bayyana cewa, mayar da shiyyar Sanatan Zamfara ta Arewa saniyar ware inda ya fito barazana ce ga dimokuraɗiyya a jihar, don haka akwai buƙatar dawo da tsarin mulkin karɓa-karɓa a shekarar 2027 a jihar.
Dr. Shinkafi ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin magoya bayansa a gidansa da ke Gusau ranar Laraba.
Ya koka da yadda shiyyar Sanatan Zamfara ta Yamma ta yi mulkin jihar tsawon shekaru 20 ba tare da ba wa sauran shiyyoyi dama ba.
“A shekarar 1999 aka zaɓi Sanata Ahmed Sani Yarima a matsayin gwamna kuma ya yi wa’adi biyu, a 2011, Sanata Abdulaziz Yari ya zama gwamna kuma ya yi wa’adi biyu, Matawalle kuma ya yi shekara huɗu kuma dukkansu ‘yan Zamfara ta yamma ne,” ya ce.
Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya ce zai tsaya takarar gwamna a shekarar 2027, inda ya ƙara da cewa zai kayar da gwamna mai ci Dauda Lawal domin ya kammala sauran shekaru huɗu na Alhaji Mahmud Aliyu Shinkafi.
“In sha Allahu zan zama gwamnan Jihar Zamfara a 2027 domin cika sauran shekaru huɗu na Alhaji Mahmud Aliyu Shinkafi domin lokacin mu ne.”
Ya bayyana cewa dole ne a yi amfani da tsarin mulkin karɓa-karɓa a 2027 a Zamfara da nufin bai wa kowane shiyya dama daidai da dimokraɗiyya.
Shinkafi ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar APC a jihar da su kasance masu bin doka da oda tare da marawa jam’iyyar baya domin ci gabanta.
