Jami’an DSS sun cafke Malam Baffa Hotoro a Kaduna

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun yi nasar cafke Malamin addinin Musuluncin nan, Malam Baffa Hotoro, da ake zargi da yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

An cafke Malam Baffa Hotoro ne a garin Kaduna a ranar Asabar kamar yadda rahotanni suqka tabbatar.

A ‘yan kwanakin nan dai malamin na wasu wa’azuzzuka tare da yin kalamai a kan Annabi SAW da ake kallon za su iya tayar da tarzoma a jihar Kano.