
Daga UMAR GARBA a Katsina
A cigaba da samun nasarar murƙushe ƴan ta’adda da jami’an tsaro ke yi a Arewa-maso-Yammacin ƙasar nan, ƴan sanda sun halaka mashahurin mai garkuwa da mutane a Katsina, wato Ɗan Ƙundu wanda ƙane ne ga ƙasurgumin ɗan ta’adda, Usman Moɗi-moɗi.
A wani gagarumin aikin dawo da tsaro da rundunar ƴan sandan Najeriya ta gudanar a jihar Katsina, ta yi nasarar kashe Ɗan Ƙundu.
Ƙundu ya shahara ta fannin ta’addanci a dajin Tsaskiya na ƙaramar hukumar Safana.
A cewar Zagazola Makama, mai sharhi kan harkokin tsaro kuma masani kan yaƙi da tada ƙayar baya a yankin tafkin Chadi, an kai harin ne a daren ranar Juma’a lokacin da Ƙundu da ƴan ƙungiyarsa suka yi yunƙurin kai hari a ƙaramar hukumar Kurfi.
Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an ƴan sanda tare da haɗin-gwiwar ƴan banga na yankin sun cafke ɗan ta’addan ne tare da mutanensa kafin su kai farmakin da suka shirya a yakin.
Musayar wuta a tsakanin jami’an tsaron da dabar ƴan ta’addar ta yi sanadin kawar da Ɗan Ƙundu da wasu ƴan dabarsa da dama.
Hakan na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan nasarar da jami’an tsaro suka samu na kawar da ƙasurgumin ɗan bindiga Halilu Sabubu daga doron ƙasa.
