Jami’ar Nasarawa za ta gudanar da bikin yaye ɗalibai karo na takwas

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Keffi

A yanzu haka babban jami’ar jihar Nasarawa dake birnin Keffi ta kammala dukannin shirye-shirye don gudanar da babban bikin gabatar da satificate wa tsofin dalibanta da suka kammala karatu a fannoni karatu daban-daban a jami’ar da ake kira convocation ceremony a turance karo na takwas a ranar Asabar.

Bikin zai shafi ɗalibai da suka yi karatu ne a matakin digiri na farko da karatun gaba da digirin farko a jami’ar.

Da take tattaunawa da manema labarai a yau Laraba a ofishin ta game da shirye-shiryen bikin, shugabar jami’ar, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta bayyana cewa rukunin ɗaliban guda uku da suka kammala karatu za a gabatar musu da satificate din su a hukumance inda ta ƙara da cewa za a kuma karrama wasu manyan mutane guda uku da lambar yabo ta digirin-digirgir kamar yadda dokar hukumar nan dake sa Ido a harkokin manyan jami’oi ta tanadar.

A cewar ta cikin waɗannan manyan mutane guda uku da za a karraman ayayin taron akwai shugaban ƙasar Tanzania Suluhu Hassan da sanannen ɗan kasuwan nan na Najeriya Abdulsamad Rabiu da wani da ba a bayyana sunansa ba.

Farfesa Sa’adstu Hassan Liman ta kuma bayyana cewa an kuma gayyato wani ƙwararren mai sharyi akan al’amuran yau da kullum wato Farfesa P. L. O. Lumumba don gabatar da lacca na musamman wato dashi da wani mai suna Dr. Umar Bindir kenan.

Ta kuma yi amfani da damar inda ta sanar cewa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule wanda shine babban baƙon jami’ar shima a nasa ran zai halarci taron mai ɗimbin tarihi wadda tace za a haɗa da bikin murnar cikar jami’ar shekaru 25 da kafuwa da sauransu.

Babbar jami’ar ta jihar Nasarawa dai tsohon gwamnan jihar, Santa Abdullahi Adamu ne ya kafa ta a shekarar 2001 a zamanin sa.

Wakilinmu a jihar ya kuma rubuto cewa a taƙaice kimanin ɗalibai sama da dubu 25 ne a matakin digiri na farko da kuma natakin digiri na biyu za a gabatar musu da satificate a hukumance a ranar Asabar mai zuwan kamar yadda shugaba Farfesa Sa’adstu Hassan Liman ta sanar a yayin tattaunawar.

By ukarofi