Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wani ma’aikacin gidan yari (Correctional Serɓice officer) Mai Babban muƙami na CCA wato Chief Correctional Assistant Abdullahi Nura dake aiki a Gidan Yari na Gusau, ya yi yunƙurin kashe kansa amma cikin taimakon Allah an ceto shi bai mutu ba.
Wani bayani daga Gidan Yarin mai ɗauke da sa hannun mai magana da hukumar Gidan Yarin ASC1 Mustapha Abubakar ya ce, da safiyar Laraba sai da Abdullahi Nura ya je wurin aiki, sai kuma ya fita ya hau kabu-kabu aka kai shi dam ɗin Baga na hanyar Wanke, kawai sai ya yi tuma ya faɗa a cikin ruwan.
Rahotanni sun nuna cewar nan take ɗan Kabu-Kabun ya yi gudu ya shaida wa ma’aikatan wurin inda suka yi ƙoƙarin ceto shi.
Hakazalika koda aka fito da shi yana sanye da uniform ɗin shi waton kayan aiki da I.D Card ɗin shi sai aka kai shi asibiti inda yanzu haka yake karɓar magani.
Sanarwar ba ta bada cikakken bayanin dalilin da ya sa wannan jami’in ya ɗauki matakin kashe kan nashi ba.
