Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Gwamnatin jihar Kebbi ta biya Naira billiyan ɗaya da rabi ga waɗanda aikin tagwayen hanyar da ta ratsa garin daga Sakkwato zuwa Yawuri ya shafa.
Shugaban kwamitin biyan diyyar gidaje da shagunan Malam Aliyu Maude ya bayyana cewa wannan aikin aƙalla ya shafi mutane ɗari biyu da talatin da shida (236) da suka haɗa da masu gidaje da shaguna.
Ya bayyana cewa bayan an biya kowa diyyar ginin sa gwamnatin jihar ta baiwa kowane daga cikin su watanni biyu don su nemi wani waje kafin kwanakin su cika wanda shi ne zai baiwa kamfanin da zai gudanar da aikin damar aiwatar da ayyukansa cikin lokaci.
Ya bayyana cewa yin wannan aikin titin zai rage cinkoso da kuma haɗurra da ke haddasa salwantar dukiyoyi wani lokacin har ma da rayuka kuma zai ƙara bunƙasa tattalin arziki.
Sarkin Kabin Jega, Alhaji Muhammad Arzika Bawa ya yaba wa gwamnan jihar Malam Nasir Idris bisa ga aiwatar da wannan aikin da suka daɗe suna fatar samu.
Basaraken ya yi kira ga al’umma da su baiwa wannan aikin cikakken haɗin kai don ganin an sami nasarar kammala shi a cikin lokacin da aka shata wanda ba shakka zai ƙara bunƙasa tattalin arziki kamar yadda aka san mutanen garin Jega mutane ne masu bin doka da son zama lafiya.
