Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An tabbatar da mutuwar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, fitaccen mai tasiri a kafafen sada zumunta na jihar Kaduna da ya ɓace shekaru shida da suka gabata, kamar yadda jaridar Manhaja ta ruwaito.
Tabbatar da hakan ya biyo bayan kammala wani bincike mai zaman kansa ƙarƙashin jagorancin mai sharhi kuma mai fafutuka, Damilola Adekunle.
An yi garkuwa da Dadiyata ne a gidansa da ke Barnawa, Kaduna, a ranar 2 ga watan Agusta, 2019. ɓacewarsa ta tada hankulan jama’a a faɗin ƙasar, kuma ana kyautata zaton cewa yana da alaƙa da siyasa, domin ya shahara da sukar jami’an gwamnati da kuma goyon bayan tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso.
A wani saƙo da ta wallafa a Facebook ranar Laraba, Adekunle ta bayyana sakamakon binciken nata:
Ta rubuta “A cikin nauyin zuciya nake sanar da cewa bayan cikakken bincike na iya tabbatar da cewa Idris Abubakar, wanda aka fi sani da Dadiyata ya rasu a hukumance. An kashe Dadiyata,” ta rubuta.
Wannan fallasa na zuwa ne jim kaɗan bayan Adekunle ta ƙaddamar da biyan zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 10 a ranar 4 ga Mayu, 2025, don ƙarfafa gwiwar mutane su fito da ingantattun bayanai game da makomar Dadiyata.
“Ina ƙaddamar da tukwicin Naira miliyan 10 domin baiwa duk wanda zai iya ba ni bincike na gaskiya kan abin da ya faru da Abubakar Idris (da aka fi sani da Dadiyata), idan kun san abin da ya same shi, ya mutu ko a raye, don Allah ku tuntuɓeni,” inji ta.
Tun daga lokacin da aka sace shi, an bar iyalan Dadiyata da mabiyansa cikin duhu. Shari’ar tasa ta ɗauki hankalin ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International a Nijeriya, inda ta sha yin kira ga gwamnati da ta bayar da amsoshi tare da tabbatar da bin diddigin lamarin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto dai, ɓangaren gwamnatin da jami’an tsaro ba su fitar da wani ƙarin haske ba akan batun.
