Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Attajirin da ya yafi kowa kuɗi a Nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya yi murabus daga shugabancin kamfanin sukari na Dangote.
Attajirin ya ajiye aiki a matsayin Shugaban Kamfanin ‘Dangote Sugar Refinery’, lamarin da ya kawo ƙarshen shugabancinsa na shekaru 20.
Sakataren kamfanin, Temitope Hassan shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce, ritayar tasa za ta fara aiki daga ranar 16 ga Yuni, 2025 domin ba sabon shugaban damar fara aiki.
Dangote ya jagoranci kamfanin tun shekarar 2005, an danganta shi da kawo sauyi da tsarin kamfanin zuwa jagora a kasuwar sukari ta Nijeriya.
Sanarwar ta ce, “Dangane da ƙa’idojin nagartaccen shugabanci da shirin samar da magaji, ‘Dangote Sugar Refinery’ na sanar da ritayar Alhaji Aliko Dangote.
Sanarwar ta ce, ƙarƙashin jagorancinsa an aiwatar da manyan ayyukan bunƙasa noma a Adamawa, Taraba da Nasarawa domin ƙara samar da sukari a gida.
A kwanakin baya, Attajirin ya yi alƙawarin zuba hannun jari a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas domin inganta tattalin arziki.
Dangote da Tony Elumelu sun yi alƙawarin zuba jari musamman a bangarorin noma da kuma makamashi.
Attajiran sun bayyana hakan ne yayin taron Taravest da aka gudanar a Jalingo, inda suka yaba wa kyakkyawan yanayin kasuwanci na jihar.
Taron ya samu halartar manyan mutane ciki har da Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III.
Hukumar ta bayyana cewa an nada Arnold Ekpe, Darakta mai zaman kansa, a matsayin sabon Shugaban Hukumar ‘Dangote Sugar Refinery’ daga 16 ga Yuni, 2025.
“Bayan tantancewa mai kyau da tsari, mun naɗa Arnold Ekpe a matsayin sabon Shugaban Hukumar ‘Dangote Sugar Refinery’.
“Muna maraba da Ekpe a matsayin sabon shugaba, tare da godewa Alhaji Dangote bisa nagartaccen aiki da jajircewar da ya nuna,” inji sanarwar.
Ekpe gogaggen ma’aikacin banki ne kuma tsohon Shugaban Ecobank, mai ƙwarewa a harkokin jagoranci da aiki a manyan hukumomi.
