Jam’iyyunmu ba ƙungiyoyin ta’addanci ba ne – Gwamnatin Tarayya ga Kotun Kanada

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da hukuncin wata kotun tarayya a ƙasar Kanada na ayyana wasu jam’iyyun Nijeriya a matsayin abinda ta kira da ƙungiyoyin ta’addanci, inda Gwamnatin Nijeriyar ta ce ba za ta amince da haka ba domin ƙarya ne mara tushe da aka jingina musu a harkokinsu na cikin gida.

Lamarin ya samo asali ne a lokacin da wani ɗan Nijeriya mai suna Douglas Egharevba ya je Kanada a watan Satumban 2017, inda ya nemi zama ɗan gudun hijira a ƙasar a ƙarƙashin dokokin bada kariya ga harkokin shige da fice da gudun hijira.

Akan haka ne kotun Kanadar ta zargi wasu daga cikin jam’iyyun siyasa na Nijeriya da ta’addanci a madadin ware wani ɓangare na al’ummar ƙasar.

Daga cikin jam’iyyun da ta lissafo akwai wadda ta samar da zaɓaɓɓun shugabannin ƙasa guda uku a Nijeriya, wato PDP, a cewarta, kowane ɗan jam’iyyar ka iya zama ɗan ta’adda.

Saidai, Gwamnatin Tarayya a wata sanarwa daga Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ta ƙaryata hukuncin da cewa Nijeriya ƙasa ce mai cikakken ƴanci da ke aiki da dokokin da suke gudanar da harkokin siyasarta.

Don haka jingina wa jam’iyyun siyasarta ta’addanci ba tare da ƙwararan hujjoji ba, ƙoƙarin ruɗar da al’umma da rage darajar cibiyoyin dimukraɗiyyar ƙasar ne wanda ka iya haddasa fitina.

Saboda haka gwamnatin ta kirayi hukumomin Kanada da su gaggauta janye waɗannan kalamai marasa kima da ƙaurace wa dukkan ababen da za su janyo a fassara siyasar Nijeriya ta munanan fuskoki.

By Babaji