
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da ake shiga sabuwar kakar ƙwallon ƙafa a ƙasashen nahiyoyi daban-daban, Hukumar Gudanarwar Wasannin Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa-da-Ƙasa IFAB, ta shirya wasu sabbin dokoki da za a riƙa amfani da su a wasanni daga sabuwar kaka.
Tuni aka fara amfani da su a wasannin FIFA Club World Cup na 2025, wato gasar zakarun Nahiyoyi da aka yi a Amurka, wanda ƙungiyar Chelsea ta lashe.
Don haka, akwai dokoki guda shidda da IFAB ta samar da suka dace kowane ɗan kallo ya sani game da kakar ta 2025/2026.
Daga yanzu, masu tsaron gida za su riƙa riƙe ƙwallo ne na tsawon daƙiƙu takwas kaɗai. Idan ya wuce haka, za a bai wa ɗaya ƙungiyar da suke wasa da ita damar bugun tazara daga gefe, wato ‘coner kick’ a madadin bugun tazara da aka saba gani a baya. Haka kuma ba za a bai wa golan kati ba har sai ya cigaba da karya dokokin.
Na biyu, kyaftin ne kaɗai wanda aka amince ya riƙa yi wa alƙalin wasa magana a yayin da ake tsaka da wasa. Idan har gola shi ne kyaftin ɗin, wajibi ne a samar da ɗan wasa ɗaya da zai riƙa magana a madadinsa yayin wasan. Duk ɗan wasan da ya tunkari alƙalin wasa musamman ta rashin girmamawa, akwai yiwuwar ya samu kati ruwan ɗorawa.
Na uku, babu rikitarwa game da wane ɓangare zai karɓi ƙwallo yayin da aka tsayar da wasa. Za a bai wa ƙungiyar da ke riƙe da ƙwallon ne a lokacin da aka tsayar da wasan, sannan idan ƙwallon ba ta cikin zagayen yadi 18, waton kewayen fenareti. Idan kuma aka rasa ganewa, sai ƙungiyar da ta taɓa ƙwallon a ƙarshe kafin a tsayar ta karɓi ƙwallon.
Abu na huɗu, idan aka samu kuskuren taɓa ƙwallo a wajen fili daga koci ko ɗan wasan benci ko kuma ɗan wasan da aka bai wa jan kati, to za bai wa ɗaya ƙungiyar damar bugun tazara, amma ba za a bada kati ba.
Sannan, abu na biyar shi ne, akwai yiwuwar a riƙa sanar da hukuncin VAR ta ansakuwwa, ta yadda masu kallo za su ji abinda aka yanke daga bakin alƙalin wasa idan ya so domin tabbatar da adalci.
Abu na ƙarshe game da bugun fenareti, idan ɗan wasa ya buga ƙwallon sau biyu bisa kure, wato idan ya doke ta sai ta taɓa ɗaya kafarsa da ba da ita ya buga ba kuma ta shiga raga, to za a sake bugawa. Idan kuma ba ta shiga raga ba, za a bada bugun tazara ga ɗaya ɓangaren.



