Zaɓen Kano: Shirye-shirye sunyi nisa wajen fara jefa ƙuri’a a ƙananan hukumomin Ghari da Ɓagwai

Spread the love

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Yanzu haka shiri yayi nisa dangane da zaɓen cike gurbi da ake gudanarwa a wasu ƙananan mazaɓu na ƙaramar hukumar Ɓagwai na ɗan majalisar jiha da ke Jihar Kano.

Ɗaya daga cikin mazaɓun sun haɗa da mazabar Kiyawa dake ƙaramar hukumar Ɓagwai, inda a cikin hotunan nan ke nuna al’umma sun hau layi za a fara tantance su dan su fara jefa ƙuri’a.

Haka kuma suma a garin ƴan kifi da ke mazaɓar Ƴan Dadi a yankin ƙaramar hukumar Ghari da a ka fi sani da (KUNCHI) suma sun hau layi dan fara gudanar da zaɓen wanda suke da ra’ayi.

By ukarofi