Janar Musa ya goyi bayan ƙudirin bai wa jami’an tsaro damar kaɗa ƙuri’a da wuri

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Laftanar Janar Christopher Gwabin Musa, ya bayyana matuƙar goyon bayansa ga wasu muhimman ƙudirorin doka guda biyu da aka tsara don yin tasiri sosai ga walwala da iya aiki na Rundunar Sojin Nijeriya.

Wannan ƙudiri na nufin baiwa jami’an soji, hukumomin tsaro da muhimman ma’aikatan zaɓe damar kaɗa ƙuri’a da wuri a babban zaɓe. A halin yanzu, sama da jami’ai miliyan biyu ne ake tura su ayyuka a wuraren daban-daban, inda ba za su iya kaɗa ƙuri’a ba saboda ayyukan da aka ba su. ƙudirin yana neman magance wannan lamari.

Ya bayyana hakan ne a ziyarar da Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua ya kai Hedikwatar Tsaro da ke Abuja.

Sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ta ce ziyarar Sanata Yar’adua ta kasance ne domin yi wa Janar Musa bayani kan ƙudirin dokar da ke gaban majalisar dokokin ƙasar a halin yanzu, wanda ke neman gabatar da fara kaɗa ƙuri’a da wuri ga sojojin Nijeriya, da sauran hukumomin tsaro, da kuma muhimman ma’aikatan zaɓe.

Da yake yin haɗin gwiwa da ƙungiyar farar hula ta Yiaga Africa, Sanata Yar’adua ya bayyana cewa an tura kimanin jami’ai miliyan biyu wuraren ayyuka daban-daban a babban zaɓen da ya gabata, amma abin takaici an hana su haƙƙoƙinsu saboda yanayin ayyukansu. ƙudirin da aka gabatar yana da nufin gyara wannan giɓin ta hanyar baiwa waɗannan jami’ai masu muhimmanci damar kaɗa ƙuri’unsu gabanin babban zaɓe.

Sanatan ya miƙa goron gayyata ga hedikwatar tsaro da su gabatar da matsayinsu a yayin taron sauraren ra’ayoyin jama’a kan wannan muhimmiyar doka, tare da jaddada muhimmancin shigar da su.

Bayan shirin kaɗa ƙuri’a da wuri, Sanata ‘Yar’aduwa ya kuma sanar da CDS wani muhimmin ƙudiri na biyu, wanda tuni ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa. Wannan dokar na da nufin samar da wasu hanyoyin samar da kuɗaɗe masu ɗorewa ga Sojojin Nujeriya. Sanata ‘Yar’adua ya buƙaci hedkwatar tsaro da ta sa baki a cikin taron sauraron ra’ayin jama’a da za a yi na wannan ƙudiri shi ma.

A nasa martanin, Janar Musa ya miƙa godiyarsa ga Sanata Yar’adua bisa ɗaukar nauyin waɗannan ƙudirori guda biyu masu tasiri waɗanda kai tsaye suka yi magana kan inganci da jin daɗin rundunar.

Janar Musa ya bai wa Sanatan tabbacin samun cikakken goyon baya da haɗin kan hedkwatar tsaro, tare da tabbatar da shirye-shiryen sojoji na taka rawar gani a cikin tarukan sauraren ra’ayoyin jama’a da kuma ba da duk wani bayanan da suka dace don tabbatar da nasarar zartar da dokokin biyu.

Hedikwatar tsaro ta jaddada ƙudirinta na ci gaba da yin duk wasu tsare-tsare don ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyyar Nijeriya da kuma inganta ayyukan rundunar sojin Nijeriya.

By ukarofi