Yadda aka kama mai garkuwa da mutane yana tsaka da cin kasuwar shanu a Neja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An kama ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi da yin garkuwa da mutum uku a ƙauyen Daku da ke Gwagwalada Abuja lokacin da yake tsaka da cin kasuwar shanu ta Izom da ke Guraran jihar Neja.

Rahotanni sun ce a ranar tara ga watan Yunin 2025 ce dai aka sace wasu makiyaya su biyu da wani direba a kusa da ƙauyen na Daku.

An sace mutanen ne lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar ta Izom.

Mutanen da aka sace ɗin dai a wancan lokacin sai da suka biya kuɗin fansa har Naira miliyan 15 kafin su shaƙi iskar ’yanci.

Wani ɗan ƙungiyar sintiri ta bijilan a yankin, Ishaku Daniel, ya ce an cafke wanda ake zargi da garkuwa da mutanen ne wajen misalin ƙarfe 4:00 na yamma a kasuwar bayan ɗaya daga cikin waɗanda ya sace ya gane shi.

Ishaku ya ce an kama mutumin ne sanye da dogayen kaya lokacin da ya shigo kasuwar domin yin sayayya.

Ya ce nan take ’yan sintirin da ke kasuwar suka cika hannu da shi, duk da cewar jama’ar gari sun so su halaka shi a nan take.

Ya kuma ce ’yan sintirin sun samu fakiti-fakitin sigari da tiramol da maganin tari da kuma wiwi a cikin buhun wanda ake zargin.

Ishaku ya ce daga bisani sun miƙa shi ga jami’an tsaro da suka je kasuwar daga Lambata a jihar ta Neja.

Shi ma wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da kama mutumin, inda ya ce tuni ya amsa laifinsa yayin da ake ci gaba da bincike a kan lamarin.

Sai dai yunƙurin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin ’yan sandan jihar ta Neja, SP Wasiu Abiodun, a kan lamarin ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

By ukarofi