Jaridar The Guardian: Amurka na da tarihin cin zarafin lafiyar fursunoni masu launin fata

Daga CRI HAUSA

Jaridar The Guardian ta ƙasar Birtaniya ta ruwaito cewa, gwajin maganin ivermectin a gidan yarin Arkansas, ya haska daɗaɗɗen tarihin cin zarafin lafiya da Amurka ke yi wa al’ummomi masu launin fata.

Rahoton jaridar ya bayyana cewa, a watan Augustan bara, an yi wa fursunoni 4 dake gidan yarin gundumar Washington dake Arewa maso yammacin Arkansas amfani da ivermectin wajen maganin COVID-19 ba tare da saninsu ba, wanda magani ne da ake amfani da shi ga dabbobin da ake kiwonsu a gida.

Cibiyar kandagarki da taƙaita yaduwar cututtuka ta Amurka da hukumar tantance ingancin abinci da magunguna ta ƙasar, sun yi gargaɗi game da illolin dake tattare da amfani da ivermectin wajen maganin COVID-19, kuma amfani da shi ya sa fursunonin fama da matsaloli, ciki har da ta gani da amai da gudawa.

Rahoton ya nanata cewa, abun da ya faru a gidan yarin, maimaici ne na mummunan tarihin wariyar launin fata na Amurka, bisa la’akari da cewa gwajin bisa tilas kan fursunonin Arkanas, ya tunantar da tarihin cin zarafin lafiya da hukumomin Amurka ke yi wa al’ummomi ko fursunoni masu launin fata.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha