Kisan gillar matar aure a Kano: Ganduje ya bada umurnin gaggauta bincike

Daga IBRaHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci jami’an tsaro da su gaggauta bincike da kamo waɗanda su ka kashe wata matar aure mai suna Rukayya Mustapha a cikin gidanta da ke unguwar Danbare, Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Kano.

Gwamnan ya bada umarnin ne a Litinin da ta gabata lokacin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan marigayiyar a unguwar Ɗorayi dake Ƙaramar Hukumar Kumbotso a jihar.

Hakan na cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamna, Hassan Musa Fagge ya fitar, Ganduje wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya ce gwamnatinsa ta duqufa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano.

”Cikin tsananin kaɗuwa mu ka samu labarin rasuwar Marigayiya Rukayya Mustapha. Ina mai tabbatar muku da cewa ba za mu bar wananan abun haka kawai ba, dole sai an nemo waɗanda su ka aikata wannan mummunan aiki,” inji Ganduje.

“A madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano, ina Allah wadai da wannan aika-aika tare da addu’ar Allah ya jiƙan ta ya sa tana Jannatul Firdaus tare da bai wa ‘yan uwanta haƙurin jure rashin,” inji Ganduje.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bayyana cewa kawo yanzu an kama mutane 5 da ake zargi, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin zaƙulo waɗanda suka kashe matar.

Ya kuma yi nuni da cewa, waɗanda suke  ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ne ke aikata irin waɗannan laifuffuka, shi ya sa suke kama duk waɗanda suke yin safarar miyagun ƙwayoyi domin daƙile sake afkuwar irin lamarin.

Kwamishina Dikko ya kuma bayar da tabbacin cewa, hukumomin tsaro za su ruɓanya ƙoƙarinsu na ganin ba a sake samun faruwar irin waɗannan laifuka ba nan gaba.

Daga cikin tawagar gwamnatin dai akwai Daraktan Hukumar ‘Yan Sanda na Farin Kaya, DSS Alhassan Muhammed da sauran kwamishinoni da jami’an gwamnatin na jihar ta Kano.