Jarumi Hanks ya tayar da ƙura bayan fitar bidiyon sa zaune gefen hanya a Abuja 

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Sabon bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya sake jefa masoya fina-finan Nollywood cikin damuwa bayan an hango fitaccen jarumi Hanks Anuku zaune shi kaɗai a gefen wata hanya a Abuja.

Bidiyon ya fara yaɗuwa ne bayan wani mai amfani da shafin X mai suna Anthony Ehilebo ya wallafa shi, yana mai cewa shi da kansa ya ci karo da jarumin a yankin Wuse 2 da ke Abuja. A cikin bidiyon, an ga Hanks Anuku zaune a kan ciyawa da ke gefen hanya yana riƙe da wani abu mai kama da kofi.

Da yake wallafa bidiyon, Ehilebo ya yi ikirarin cewa yanayin da ya tarar da jarumin ya tayar masa da hankali, yana mai cewa Hanks Anuku na buƙatar taimako, musamman ta fuskar kula da lafiyar ƙwaƙwalwa.

Sai dai ba a daɗe ba lamarin ya haifar da muhawara, inda wasu masu amfani da kafafen sada zumunta suka yi zargin cewa watakila bidiyon daga wurin ɗaukar fim ne, suna tuna irin rahotannin da suka taɓa fitowa a baya game da jarumin.

Amma Ehilebo ya yi watsi da wannan zargi, yana mai jaddada cewa ba a wurin ɗaukar fim ya gan shi ba.

“Ni da kaina na ɗauki wannan bidiyon,” inji shi.

Haka kuma, wata shaidar gani da ido ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su haɗa kai wajen tallafa wa fitaccen jarumin, tana mai cewa bai kamata a ce mutum mai irin gudunmawar da Hanks Anuku ya bayar ga masana’antar Nollywood yana cikin irin wannan hali ba.

Sai dai duk da yaɗuwar bidiyon da zarge-zargen da ke yawo a kafafen sada zumunta, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wata sanarwa daga Hanks Anuku ko wakilansa da ke tabbatar ko musanta abin da ke cikin bidiyon. Saboda haka, ba a tabbatar da ainihin halin da jarumin yake ciki ba, yayin da cece-kuce kan bidiyon ke ci gaba da ɗaukar hankali.

By ukarofi

Leave a Reply