Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Fitaccen ɗan siyasa kuma attajiri na yankin Tangale-Waja, a Gombe ta kudu Hon. Jerry Joseph Damara, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Damara, wanda shi ne shugaban kamfanin Mesotho Group da Kugbo International Market, ya miƙa katin shaidar mambobinsa na APC ga gwamna Muhammad Inuwa Yahaya a gidan gwamnatin Gombe.
Ya ce ya yanke shawarar hakan ne sakamakon ci gaban da gwamnatin Inuwa Yahaya ta samu da kuma salon shugabancin sa na haɗa kan al’umma.
A nasa jawabin, Gwamna Yahaya ya bayyana wannan sauyi a matsayin babban ci gaba ga jam’iyyar APC, yana mai cewa Damara babban jigo ne a siyasa da zai ƙarfafa jam’iyyar a Gombe ta Kudu.
