Jihohin Nijeriya biyar da aka fi kashe mutane a 2025 – Rahoto

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da suka fi ci wa Nijeriya tuwo a ƙwarya, inda matsaloli da dama masu alaƙa da tsaro ke ci ga da yi wa ƙasar katutu.

Matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta sun haɗa da hare-haren masu iƙirarin jihadi da ‘yan bindiga ko ‘yan fashin daji masu satar mutane domin neman kuɗin fansa da rikicin manoma da makiyaya.

Kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, mai nazari kan al’amuran tsaro a Nijeriya da ƙasashen yankin Sahel ya ce an samu raguwar matsalar tsaron a shekarar da ta gabata idan aka kwatanta da 2024.

Cikin rahotonsa na shekara-shekara da yake fitarwa, Beacon Security ya ce an samu ragi na mutanen da hare-haren ‘yan bindiga suka kashe da waɗanda aka sace idan aka kwatanta da 2024.

Rahoton ya kuma lissafo jihohin da aka fi samun matsalolin tsaro a shekarar da ta gabatan.

Beacon Security ya yi la’akari da manyan matsalolin tsaro guda biyu, wato kisan mutane da sace su domin neman kuɗin fansa, wajen jera jihohin da suka fi samun matsalar.

Dogaro da rahoton na Beacon Security mun zaƙulo jihohin Nijeriya  biyar da aka fi samun matsalolin tsaron a 2025.

Sai dai kamfanin na Beacon ya ce duk da matsalolin tsaro da aka samu a waɗannan jihohi a 2025, an samu raguwar matsalar idan aka kwatanta da shekarar 2024.

Jihohin da suka fuskanci ɓullar matsalar a 2025

Rahoton kamfanin na Beacon Security ya kuma bayyana samun ɓullar matsalolin hare-haren a wasu jihohin ƙasar da ba a saba gani ba.

Kamfanin ya ambato jihohin Kano da Kebbi da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar da jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar ƙasar da wasu sassan yankin kudu maso yammci cikin inda aka samu ɓaullar matsalar tsaron.

Kebbi

Jihar Kebbi ta fuskanci ɓullar ƙungiyar Lakurawa, wata sabuwar ƙungiyar ‘yan bindiga da ta ƙarfafa hare-hare a 2025.

Haka kuma a shekarar 2025 wasu ‘yanbindiga suka kai hari makarantar sakandiren ‘yanmatan Maga da ke jihar tare da sace ɗalibai 25, kodayake daga bayaan sako su.

Kano

A jihar Kano kuwa an ga yadda aka samu ɓullar hare-haren ‘yan bindiga a wasu yankunan jihar da ke iyaka da jihar Katsina.

A shekarar 2025 an samu hare-haren ‘yan bindiga a ƙananan hukumomin Tsanyawa da Shanono inda suka sace mutane da dama tare da kashe wasu.

Kwara

A jihar Kwara ma da ke arewa ta tskiyar ƙasar an samu sabbin ɓullar sabbin hare-hare a wasu yankunan jihar da ba a saba gani ba a baya.

A shekarar 2025 an samu ƙaruwar hare-hare a jihar inda aka sace wasu masu ibada a wasu coci guda biyu a jihar, kodayake daga baya gwamnati ta sanar da ƙubutar da su.

By ukarofi