Jiragen yaƙi sun yi ruwan bama-bamai kan farar hula bisa kuskure a Nasarawa

Daga WAKILINMU

A ci gaba da shirinta na kakkaɓe ‘yan ta’adda a sassan ƙasa da Rundunar Sojojin Saman Nijeriya ke yi, rundunar a bisa kuskure ta yi ruwan bama-bamai a kan farar hula wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane da daman gaske.

Jaridar Peoples Gazette ta rawaito lamarin ya auku ne ranar Talata a ƙauyen Rukubi da ke kan iyakar Nasarawa da Binuwai a Ƙaramar Hukumar Doma, Jihar Nasarawa.

Wannan dai ba shi ne karon farko da jirgin yaƙin Nijeriya ke ruwan bama-bamai kan farar hula bisa kuskure a ƙasar ba.

Aƙalla mutum 47 wanda galibinsu Fulani makiyay ne aka tabbatar sun mutu sakamakon harin, inda aka kwashi waɗanda suka jikkata zuwa asibiti a Nasarawa da Binuwai.

Gwamnan jihar, Injiya Abdullahi Sule, ya tabbatar da aukuwar hakan ranar Laraba. Yana mai cewa, ana ƙoƙarin warware matsalar da sojoji.

Mai magana da yawun sojojin Nijeriya ya ce, an kai harin da nufin kakkaɓe ‘yan ta’adda ne amma ba a kan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.