Jirgin Super Eagles ya yi tangal-tangal a sama kan hanyarsu ta dawo wa Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An shiga takura na tsawon lokaci yayin da jirgin saman da ya yi jigilar ƴan wasan Super Eagles daga Afirka ta Kudu zuwa Uyo a Jihar Akwa-Ibom ya samu tsaiko, lamarin da ya tilasta masa saukar gaggawa a Luanda, Babban Birnin ƙasar Angola.

Al’amarin ya faru ne a yammacin yau Asabar, a lokacin da tawagar ƴan wasan ke shirye-shiryen karawa da Jamhuriyar Benin a wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, jirgin na ValueJet, wanda da fari ya ya da zango a Luanda domin zuba mai, ya juyo ne bayan minti 25 da barinsa birnin sakamakon wani ƙara mai ƙarfi da aka ji daga sashen ɗaya daga cikin hannayensa, wanda ya sa matuƙinsa ya fara bin tsare-tsaren gaggawa.

Baki ɗaya ƴan wasan, jami’an wasa da wakilan gwamnati sun samu ficewa daga jirgin ba tare da samun rauni daga ko ɗayansu ba.

A halin yanzu tawagar tana jiran ganin matakin da kamfanin jirgin zai ɗauka domin su samu damar kammala tafiyarsu cikin aminci.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta ƙasa NFF, ta tabbatar da faruwar al’amarin, inda ta ce jirgin ya yi saukar gaggawa ne sakamakon fashewar ɗaya daga cikin gilasansa na hango waje daga ciki.

By Babaji