
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A wani yunƙuri na tausayawa da gyara a harkar shari’a, Shugaba Bola Tinubu ya amince da yafiyar shugaban ƙasa akan mutane 175 da aka yanke wa hukunci, waɗanda daga cikinsu akwai Manjo Janar Mamman Vatsa, Farfesa Magaji Garba da Marigayi Ken Saro-Wiwa da wasu magabatan Ogoni su takwas.
Daga cikin samfurin laifukan waɗanda aka yi afuwar akwai haƙar ma’adinai ta haramtattun hanyoyi, laifukan ofis ga jami’ai, hannu a ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, na ƙasashen waje, da wasu daban-daban da suka sanya aka tasa ƙeyar masu su zuwa gidan yari.
An samu ci-gaban ne bayan shawara daga kwamitin mashawarta na shugaban ƙasa akan ikon yin afuwa, ƙarƙashin jagorancin Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi.
Ministan ya gabatar da rahoton kwamitin a yayin zaman majalisar ƙasa da Shugaba Tinubu ya jagoranta a makon da yq gabata.
A wata takarda da Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Shugaban Ƙasar ya amince da yin yafiyar ne bayan nazari akan rahoton, wanda ya nuna cewa da dama daga cikin waɗanda aka yanke wa hukunci sun yi nadama da koma wa aikata kyawawan ayyuka tare da koyon sana’o’i ko shiga Jami’ar NOUN domin neman ilimi.
Haka kuma, wasu an musu afuwar ne saboda sun manyanta da kuma waɗanda suke fama da matsalolin rashin lafiyar da ka iya kisa a kodayaushe..
Maryam Sanda Mai shekaru 37, wadda ɗaya ce daga cikinsu, an yanke mata hukuncin kisa ne tun a 2020 sakamakon samun ta da laifin halaka mijinta.
Ta shafe shekaru shida da wata takwas a gidan yarin Suleja da ke jihar Neja, inda ta samu shiga sahun waɗanda aka yi wa afuwar bayan magiya daga ahalinta.

