Juyin mulkin da aka yi Guinea-Bissau ya fi kama da wasan kwaikwayo a wajena – Jonathan

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya zargi shugaban ƙasar Guinea-Bissau, Umaro Embaló, da kitsa hamɓarar da gwamnatinsa da kansa domin gujewa faɗuwar zaɓen ƙasar da aka kammala amma ba a kai ga faɗin sakamakon zaɓen ba.

Mista Jonathan ya ce juyin mulkin ya fi kama da “wasan yara” inda ya buƙaci lallai a sanar da sakamakon zaɓen.

Tsohon shugaban ƙasar ya jagoranci tawagar dattawan Afirka ta yamma domin sa ido kan zaɓen shugaban ƙasa da ‘yan majalisu a Guinea-Bissau wanda aka yi a ranar lahadin da ta gabata.

Ya dawo gida ne a ranar Alhamis bayan juyin mulkin da sojojin suka yi.

A yayin da yake magana da manema labarai a ranar Juma’a, Janathan ya ce ba zai ayyana juyin mulkin da irin wanda aka saba yi ba, yana zargin an shirya shi ne domin dakatar da sanar da sakamakon zaɓen.

Ya ce, ba wani jagoran soji da zai bar shugaban ƙasa yana amfani da wayar hannunsa wajen magana da manema labarai alhalin yana tsare.

Jonathan ya ce shugaban ƙasar Umaro Embaló ne ya yi gaggawar sanar da an haɓɓarar da gwamnatinsa a yayin da yake iya magana da kafafen yaɗa labarai na duniya da wayarsa, wanda ya jefa masa kokwanto kan garkiyar lamarin.

“Abin da ya faru a Guinea-Bissau ya dame ni a matsayin wanda ya yi imani da dimokraɗiyya. A gaskiya ma wannan abu ya yi min zafi fiye da ɗaga waya da na yi na taya Buhari murnar lashe zaɓe alhalin ina shugaban ƙasa mai ci.”

“Abin takaici ne a wajena yadda shugaba Embaló ya sanar da yi masa juyin mulki. Wannan ba abin da za a yarda ba ne,” Jonathan ya faɗa.

“Abin da ya faru a Guinea-Bissau ba zan kira shi da juyin mulki ba. Saboda ƙarancin kalmomi zan kira abin da ya faru da wasan yara ne ta yadda shugaba Embaló da kansa ya sanar da juyin mulkin kafin sojoji su fitar da sanarwa a kan yanzu sun karɓe iko.”

“Embaló ya riga ya sanar da juyin mulkin wanda abu mamaki ne. Ba kawai sanar da juyin mulkin ba ne, har a lokacin da aka yi juyin mulkin yana amfani da wayarsa da magana da kafafen yaɗa labarai a duniya kan cewa an kama shi. Ni ɗan Nijeriya ne da ke dosar shekara 70, kuma na san yadda suke tsaron shugaban ƙasa idan suka yi juyin mulki.”

“Ba yadda za a yi su riƙa abin kamar wasa. Ba zai yiwu ba a ce an yi juyin mulki a lokacin da ake shirin sanar da sakamako, kuma a ce shugaban ƙasa na sanar da juyin mulki. Ba a inda haka ke faruwa,” inji Jonathan.

Juyin mulkin ya faru ne kwana ɗaya da hukumar zaɓen ke shirin sanar da wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a ranar Lahadi.

Zaɓen ya ƙunshi Embalo, ɗan takarar jam’iyyar Madem‑G15 da kuma abokin karawarsa Fernando Dias, ɗan takarar jam’iyyar Party for Social Renewal (PRS).

Embalo, wanda wa’adin mulkinsa zai ƙare a watan Fabarairu yana neman kafa tarihin shugaban ƙasar da ya lashe wa’adin zaɓe biyu ne a jere a tsawon shekaru 30.

“Zan zama ɗan takarar da zai maye gurbin kansa,” in ji Embalo kamar yadda aka rawaito ya faɗa a watan Maris.

Jim kaɗan bayan juyin mulkin, Embalo, ya ba da labarin cewa sojoji sun yi tsare shi a ofishinsa da ke fadar shugaban ƙasar da misalin ƙarfe 1 na rana.

Ya ce, sun yi juyin mulkin ne cikin ruwan sanyi ba tare da wata hatsaniya ba.

A ranar Alhamis ne babban hafsan sojin Embalo, Horta Inta-A, ya kama mulkin riƙon ƙwarya a matsayin shugaban ƙasa.

Inta-A ana kallon sa a matsayin wanda yake da kusanci da shugaban ƙasar wanda ya tsere zuwa ƙasar Senegal.

Sabon hafsan sojin wanda aka rantsar, Tomas Djassi, shi ma ana ganin na hannun damar shugaba Embaló ne.

Haka kuma firaministan Senegal, Ousmane Sonko, ya bayyana juyin mulkin da na ƙarya.

Jaridar Reuters ta rawaito cewa Sanko ya nemi a cigaba da gudanar zaɓen kamar yadda Janathan ya buƙata na sanar da sakamakon zaɓen.

“Abin da ya faru a Guinea-Bissau ƙire ne. Muna so a cigaba da zaɓe. Lallai ne hukumar zaɓe ta ayyana wanda ya lashe zaɓe,” ya bayyana.

Sannan haɗakar masu goyon bayan ɗan takarar hamayya, Mista Dias, ya yi Alla-wadai da juyin mulkin, yana mai cewa Embaló da abokansa ne suka haɗa kai wajen dakatar da sanarwar.

Majalisar ɗinkin Duniya ta yi Alla-wadai da juyin mulkin:

Sakatare-janar na majalisar ɗinkin duniya, António Guterres, ya yi Alla-wadai da juyin mulkin da aka yi a ƙasar Guinea-Bissau.

Guterres ya bayyana cewa juyin mulkin da watsi da “abin da mutane ke so” waɗanda suka kaɗa ƙuri’a domin zaɓen shugaban da suke so kwana kaɗan kafin juyin mulkin.

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na ɗ, Mista Guterres ya ce, ya damu da abubuwan da suke faruwa a yankin Arewa maso yamma.

Ya yi kira abin da ke faruwa a ƙasar da saɓa dokokin dimokraɗiyya.

“Duk wani watsi da zaɓin al’umma waɗanda suka kaɗa ƙuri’a cikin kwanciyar hankali a ranar 23 ga watan Nuwambar, kuma wannan abu ne da ba za a lamunta ba.”

Sannan ya buƙaci a gaggauta dawo da kundin tsarin mulkin tare da sakin dukkan jami’an da aka kama.

Juyin mulki ya sha suka daga gwamnatoci da ƙungiyoyin gamayyar ƙasashe a yammacin Afirka.

A ranar juma’a ce, ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta dakatar da Guinea-Bissau daga ƙungiyar. Ita ma haka ƙungiyar tarayyar Afirka ta ɗauki irin wannan mataki.

ƙungiyar tarayyar Afirka, “ta dakatar da Guinea-Bissau daga ƙungiyar nan take,” in ji shugaban ƙungiyar Mahamoud Youssouf.

Gwamnatin Nijeriya ta ce juyin mulkin na kawo naƙasu ga ƙoƙarin da ƙasashen ƙungiyar ke yi wajen tabbatar da amfani da kundin tsarin mulki da tsayayyen tsarin siyasa.

Ita ma ƙasar Ghana ta “nuna rashin daɗinta sosai” ga abin da ke faruwa na yin watsi da zaɓin al’ummar Guinea-Bissau.”

By ukarofi