Ka daina tunzura mutane ko doka ta yi aiki a kanka – Matawalle ga Amaechi

Spread the love

Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya gargaɗi tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, kan kalaman da ya yi na cewa ‘yan siyasa a Najeriya na mulki ne don su wawashe dukiyar ƙasa, su yi kisan gilla, da kuma su ci gaba da riƙe madafun iko.

Amaechi ya yi wannan furuci ne a wani taron ƙasa da aka shirya kan ƙarfafa dimokuraɗiyya a Najeriya, inda ake tattauna hanyoyin inganta shugabanci nagari da gaskiya a siyasa.

Tsohon gwamnan Jihar Ribas ya ce shugaba Bola Tinubu da sauran ‘yan siyasa ba za su miƙa mulki ga matasa ba sai da gwagwarmaya. Ya kuma soki yadda ‘yan Najeriya ke yarda da maganganun ‘yan siyasa cikin sauki tare da amincewa da tayin kudi daga hannunsu.

Matawalle, yayin da yake mayar da martani a wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike, ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana kalaman Amaechi a matsayin rashin hankali da kuma abin tayar da fitina.

Ya ce mulki ana samunsa ne ta hanyar dimokuraɗiyya ba ta hanyar tsoratarwa, tashin hankali, ko kuma rashin bin doka da oda ba.

Matawalle ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu na kokarin tabbatar da zaman lafiya da kare darajar dimokuraɗiyya da tsaro ga dukkan ‘yan Najeriya.

“Tsohon mai riƙe da muƙamin gwamnati bai kamata ya yi irin waɗannan kalamai marasa hankali da ke iya haddasa rikici ba,” in ji Matawalle.

Ya kuma yi gargaɗi cewa gwamnati ba za ta amince da duk wani yunƙuri na tada zaune tsaye ko rura wutar tashin hankali a ƙasar ba.

“Bari in bayyana sarai: hukumomin tsaro suna cikin shirin ko ta kwana. Duk wanda aka samu yana tayar da zaune tsaye ko ƙoƙarin haddasa fitina a kasar nan zai fuskanci hukunci mai tsanani.

“Ba za mu lamunci kowanne irin kalami da zai iya haddasa rabuwar kai ko rikici a ƙasar nan ba. Gwamnati ba za ta kyale kowa ya tayar da tarzoma ko ya hana zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya ba,” in ji shi.

By ukarofi