Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS, ta gargaɗi ƙasashen Afirka da su guji rumgumar ƙirƙirarriyar basira ta AI, musamman a harkokin majalisar, tare da jaddada buƙatar yin taka tsantsan da fasahar.
An yi wannan kiran ne a taron ƙara wa juna sani na majalisar ECOWAS na 2025 da aka gudanar a garin Fatakwal na jihar Ribas. ƙwararru da ‘yan majalisa sun yarda cewa yayin da AI ke ba da babbar dama, dole ne ɗan dama ya yi wasu abubuwan da kansa.
A yayin tattaunawar, ‘yan majalisar da suka haɗa da Guy Marius Sagna (Francophone) da Laadi Ayamba (Anglophone) sun yarda cewa galibin ‘yan majalisar ba su da isasshen ilimin fasahohin zamani, suna mai jaddada buƙatar wayar da kan jama’a a hankali. Sun yi gargaɗin cewa rumgumar AI da wuri zai iya kawo lahani fiye da alfanu, musamman a wuraren aiki.
Ayamba, yana ƙara nuna damuwa game da illolin dogaro da fasahar zamani a zamantakewa, ya ce, “Yaranmu sun riga sun rasa muhimmiyar alaƙar zamantakewa saboda yawan amfani da waya, kuma yanzu muna cikin hanzari zuwa AI. Bai kamata mu runguma ta makance ba tare da yin la’akari da tasirinsa na dogon lokaci akan al’adunmu, tunaninmu, da kuma tsararraki masu zuwa. AI kyakkyawan tunani ne, amma bari mu gaggauta sannu a hankali.”
Sauran ‘yan majalisar sun jaddada cewa, ‘yan majalisar, waɗanda ake zabar su ne domin kare al’ummarsu, dole ne su guji yin doka ta hanyoyin da za su iya jefa jama’a cikin haɗari. Sun yi kira da a yi kiraye-kiraye, har ma a yankunan karkara, kafin buɗe AI. Sun ƙara da cewa ƙalubalen shugabanci na Afirka, da suka haɗa da cin hanci da rashawa da cibiyoyi masu rauni, sun sa nahiyar ta yi rashin shiri don karɓe AI.
