Saudiyya ta gindaya sabbin sharuɗɗan zuwa aikin Hajji

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tuni dai aka fara bayyana fargaba bayan da ƙasar Saudiyya ta ɓullo da wasu sabbin tsauraran ƙa’idoji ga maniyyata aikin Hajjin bana.

Saudiyya ta tsaya kai da fata wajen yin aiki da sababbin ƙa’idojin, wanda idan ta tabbata da yawa daga cikin maniyyatan Nijeriya ba za su samu damar zuwa sauke farali a aikin Hajjin da ke tafe ba.

Yanzu haka dai wasu jami’an hukumar alhazan Nijeriya suna ƙasar mai tsarki, domin tattauna yadda za a fuskanci sababbin matakan.

Fatima Sanda Usara, mai riƙon muƙamin daraktar yaɗa labarai ta hukumar alhazan Nijeriyar, wato NAHCON ce, ta shaida wa BBC cewa, babban matakin da Saudiyya ta ɗauka shi ne da zarar an daina karɓar kuɗin aikin hajji, to ba za su koma baya ba, ama’ana babu wanda za a karɓi kuɗinsa daga baya.

Ta ce,” A bana Saudiyya ta bayyana cewa zuwa 12 ga watan Oktoban 2025, tana so a fara tura sunayen waɗanda suka biya kuɗinsu na aikin hajjin da ke tafe, sannan mahukuntan Saudiyyan sun ce duk wani kuɗi ko kwangila da za a bayar a game da abubuwan da suka shafi harkokin sufuri a Saudiyyan wajen jigilar alhazai a ƙasa mai tsari, to ya kamata a kammala komai zuwa ranar 12 ga watan Oktoban.”

Mai riƙon mukamin daraktar yada labarai ta hukumar alhazan Najeriyar, ta ce,” Ta fuskar kiwon lafiya kuma, mahukuntan Saudiyya sun ce a bana duk wanda zai je aikin hajji to dole sai an tabbatar a asibiti cewa yana da ƙoshin lafiya, sannan duk wani mai ciwon koɗa ko hanta da sauran cutuka masu tsanani, to ba za su je aikin hajjin a bana ba.”

Ta ce,” Wannan mataki kuma ya shafi masu juna biyu da masu taɓin hankali. Sannan duk mutumin da ke ɗauke da wata cuta wadda za a iya yaɗa ta kamar tarin fuka da Ebola da cutar zazzaɓin lasa, shi ma ba zai je aikin hajjin bana ba muddin aka tabbatar da cutar.”

Fatima Sanda Usara, ta ce,” A cikin cutukan da suka lissafa babu hawan jini da ciwon siga, to amma a lokuta da dama ana cewa masu irin waɗannan cuta su riƙa tafiya da maganinsu da kuma shaidar cewa kana da cutar.”

Ta ce,” Mahukuntan Saudiyya, sun ce sun ɗauki waɗannan matakan ne domin tabbatar da cewa an kammala shirye-shiryen da suka kamata domin su san iya adadin mutanen da za su je aikin hajjin daga kowacce ƙasa don a shirya abin da ya dace.

“Saudiyya a kodayaushe tana so ta san iya adadin mutanen da za su halarci aikin hajji a kowacce shekara domin yin tanadin duk abin da ya kamata, shi ya sa take so a gama komai a kan lokaci don gudun fuskantar matsala ko kuma suma kansu alhazan su rasa samun kulawar da ta dace,” inji ta.

By ukarofi