Kai maƙaryaci ne, Gwamna Abba ga Baffa Bichi

Spread the love

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya mayar da martani mai zafi kan zargin da tsohon sakataren gwamnatin Jiha, Baffa Bichi, ya yi masa, yana mai cewa dukkanin ikirarin ƙarya ne da aka ƙirƙiro domin ɓata masa suna da yaudarar jama’a.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin, ya fitar a ranar Lahadi, Gwamna Yusuf ya bayyana Bichi a matsayin “maƙaryaci marar kunya” wanda maganarsa bata cancanci kulawa ba.

Gwamnan ya ƙaryata zargin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana karɓar Naira biliyan biyu a kowane wata daga gwamnatin jihar Kano. Ya bayyana wannan zargi a matsayin “babin ƙarshe na rashin gaskiya da raɗaɗin siyasa”.

Ya ce Kwankwaso ba ya tsoma baki a cikin kuɗaɗen gwamnati kuma bai taɓa neman ko sisin kobo daga gwamnatin sa ba.

Haka kuma, Gwamna Yusuf ya soki lokaci da dalilin da yasa Bichi ya fito da wannan zargi, inda ya ce ya yi shiru tsawon watanni yana aiki a gwamnati kafin a kore shi saboda gazawa da sakacin aiki. Ya ce, “Idan kana da gaskiya da amana, da ka faɗi wannan tun da kana ofis, ba sai an kore ka ba.”

A ƙarshe, Gwamnan ya jaddada ƙudurin sa na gudanar da mulki na gaskiya da riƙon amana, yana mai kira ga al’ummar jihar Kano da su yi watsi da “hayaniyar ’yan siyasa da suka rasa kima”.

By ukarofi