Yobe: Boko Haram sun kashe jami’ai huɗu a farmakin da suka kai wa sojoji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Asabar ne wasu mahara da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne suka farmaki sojojin ‘Task Force’ na Birget ta 27, dake yankin Buni Yadi na Ƙaramar Hukumar Gujba a Jihar Yobe, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe jami’ai huɗu da ɗaiɗaita wasu kayayyaki.

Hakan ya faru ne ƙasa da kwana ɗaya da gwamnonin Arewa maso Gabas suka haɗu a jihar da nufin samar da hanyar magance matsalolin ta’addanci a shiyyar ta hanyar amfani da salo na musamman.

Buni Yadi nan ne mahaifar Gwamnan jihar, Mai Mala Buni, wanda ke da nisan kilomita 65 daga Babban Birnin jihar, Damaturu.

Wani jami’i da ya samu tsere wa harin, ya shaida wa manema labarai cewa mayaƙan sun farmake su ne da misalin ƙarfe 2 na dare, inda suka kori sojoji daga Birget ɗin tare da ƙone baki ɗaya kayan aikin da aka sanya a wajen.

Haka ma wani soja da ya samu tsira, ya bayyana cewa mayaƙan sun kai harin a wani adadi mai yawa tare da jefa ababen fashewa da yin harbe-harbe a yayin da suke ƙoƙarin shiga sansanin sojojin.

Tun a ranar ne Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta tabbatar da aukuwar lamarin tare da cewa jami’an Atisayen ‘Haɗin Kai’ sun fara ƙoƙarin daƙile harin ISWAP a yankin, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Facebook.

By Babaji